Home Back

Saudiyya Ta Raba Dabino Ga Makarantu, Gidajen Marayu Da Asibitoci A Kano

leadership.ng 2024/5/6
Saudiyya Ta Raba Dabino Ga Makarantu, Gidajen Marayu Da Asibitoci A Kano

Gwamnatin Saudiyya, ta hannun babban jami’in Jakadancinta da ke Jihar Kano, ta ba da gudunmawar dabino ga Masallatan Juma’a, makarantun islamiyya, gidajen marayu da asibitoci a jihar. 

Katan 3000 ne na dabino gwamnatin Jihar Kano ta karba a ranar Laraba, wanda sakataren gwamnatin jihar, Baffa Bichi ya wakilci gwamna Abba Kabir Yusuf.

A lokacin da Bichi ke karbar dabinon a madadin wadanda aka bai wa, ya bayyana farin cikin gwamnatin Kano da irin gudunmawar da ta ke samu daga Saudiyya.

“Muna godiya ga Allah da irin wannan taimako da gudunmawa da muke samu daga jama’a da gwamnatin Saudiyya.

“Za mu tabbatar cewa wannan dabino da aka raba sun iske wadanda aka yi domin su. Za a yi rabon dabinon kamar yadda aka tsara a rubuce” in ji Bichi.

Yayin da yake mika dabinon, babban Jami’in Jakadancin Saudiyya da ke Kano, Khaleel Ahmad Adamawiy, ya ba da tabbacin cewa gwamnatin Saudiyya ta karkashin hukumar ba da taimako da tallafin gaggawa na masarautar kasar, na ba da taimako da yawa a Nijeriya a bangarori da dama.

“Nan kusa a cikin shekarar da ta gabata, mun gabatar da tsarin ciyarwa da mutane 48,300 suka amfana da kayan tallafin abincin a Jihar Kano da Yobe da kuma Borno inda aka kashe Dala 500,000.

“Haka kuma a Kano an ciyar da kimanin iyalai 2,056 a wannan shekarar.

“Hukumar ta gabatar da ayyukan kula da lafiya a Abuja da Legas a cikin manufarta na ba da taimako ga mabukata da kuma tsarinta na taimaka wa masu rauni domin rage musu radadin talauci.

“Wannan gudunmawa na dabino na daga cikin irin wadannan ayyuka da ake gabatarwa da sahalewar mai kula da Masallatan biyu masu tsarki, zuwa ga kasashe da ake aminci da su da suka hada da Nijeriya, domin tabbatarwa da an taimaka wa iyalai masu bukata a fadin duniya” in ji Adamawiy.

A cikin jawabinsa ya bayyana cewa kafa wannan hukumar bayar da taimako da tallafin gaggawa ta Sarki Salman a ranar 15 ga watan Mayu, 2015, tare da taimakon kasashe 175 na Majalisar Dinkin Duniya, hukumar ta kammala ayyuka da ba da taimako da aka kiyasta kudinsu ya kai dala biliyan 6.2 a kasashe 91.

Tuni gwamnatin Jihar Kano ta fara raba dabinon ga wadanda aka bayar dominsu a Jihar.

People are also reading