Home Back

Ana Tsaka da Bikin Sallah Wasu Sun Hallaka 'Yar Gidan Magajiya, Zara a Dakin Otal

legit.ng 2024/7/5
  • Rundunar 'yan sanda a Abuja ta cafke wasu mutane biyu kan kisan budurwa mai zaman kanta a dakin otal
  • Rundunar na zargin Maman Ajiya da Usman Lawal da caccakawa Zara Tua almakashi inda suka yi ajalinta
  • Kakakin rundunar 'yan sanda a Abuja, Joshephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce an fara bincike

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Rudnunar 'yan sanda a birnin Abuja ta tabbatar da cafke wasu mutane kan kisan wata budurwa mai zaman kanta.

Wadanda ake zargin Maman Aliya da Usman Lawal sun dabawa budurwar mai suna Zara Tua almakashi a otal.

Lamarin ya faru ne a otal din Galaxy Byazhin a ranar Lahadi 16 ga wata Yuni a Kubwa da ke birnin Abuja, cewar Punch.

Ana zargin daya daga cikinsu ne ya aikata laifin bayan ya shiga cikin otal din inda ya samu budurwar a ciki bayan samun sabani.

Wani mazaunin yankin kusa da otal din da ya bukaci boye sunansa ya ce budurwar ta kasance karuwa ce mai zaman kanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar ta ce an caka mata almakashi a wurare bakwai a jikinta har da cikinta inda 'yan sanda suka kwash ta zuwa asibiti.

Kakakin rundunar 'yan sanda a birnin, Joshephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce an fara bincike.

"An samu sabani tsakanin mutanen uku inda ya yi sanadin Zara wanda aka caccaka mata almakashi."
"Bayan samun rahoton, rundunar 'yan sanda ta isa wurin inda ta samu matasa sun yiwa Ajiya duka kawo wuka.
"An kwashi Ajiya da kuma Zara zuwa babban asibitin Kubwa inda likitoci suka tabbatar da cewa Zara ta rasu."

Joshephine Adeh

Asali: Legit.ng

People are also reading