Home Back

Nijeriya Za Ta Zuba Tiriliyan 2 Don Bunkasa Tattalin Arziki

leadership.ng 2 days ago
Tinubu Ya Nada Musa Aliyu A Matsayin Shugaban ICPC

Shugaba Bola Tinubu ya shirya wani yunkurin bunkasa tattalin arziki da ya kai Naira tiliyan 2 daidai da dala biliyan 1.3 don magance manyan matsaloli, ciki har da samar da abinci.

Tinubu ya umarci tawagarsa ta tattalin arziki su shirya wani tsari na zuba Naira tiriliyan biyu, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.33 don magance matsalolin da ake da su game da samar da abinci da hauhauwar farashi da kuma karfafa muhimman sassa, in ji Ministan Kudi a ranar Alhamis.

Shirin, wanda za a aiwatar da shi tare da hadin gwiwar gwamnatocin jihohi da kamfanoni masu zaman kansu, zai ware naira tiriliyan daya, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 664.45 ga harkokin noma da samar da abinci da kuma bangaren makamashi, sai wata Naira biliyan 350 domin kula da lafiya da walwalar jama’a, kamar yadda Olawale Edun ya fada wa manema labarai.

Tun bayan hawansa mulki a watan Mayun bara, Tinubu ya aiwatar da sauye-sauye da suka haɗa da rage tallafin man fetur da wutar lantarki da kuma rage darajar Naira sau biyu, a yayin da yake fafutukar kara zuba jari da kara yawan kayayyakin da ake samarwa.

Sai dai tattalin arzikin kasar ba ya samun ci gaba cikin sauri kasa da 6% a duk shekara kamar yadda ya yi fata, yayin da sauye-sauyen suka sa tashin farashin kayayyaki ya kai mafi muni a cikin shekara 28, ya kuma ta’azzara yanayin rayuwa.

Samar da abinci

“Abu na farko da shugaban ya mayar da hankali a kai shi ne samar da abinci” a cewar Edun ranar Laraba bayan da Tinubu ya kaddamar da wani gyara na tsarin tafiyar da tattalin arziki.

Edun ya ce “Jajircewa wajen samar da abinci a farashi mai rahusa da kuma samar da shi da yawa shi ne abin da Shugaban Ƙasa ya fi mayar da hankali a wannan lokaci.”

Har ila yau, shirin na son magance matsalar raguwar yawan man da ake hakowa da nufin ƙara yawansa zuwa ganga miliyan biyu a kowace rana, ta yadda za a samar da ƙarin kudaden shiga da kuma musayar kudaden waje ga tattalin arzikin kasar.

Nijeriya ta dogara ne da man fetur wajen samun fiye da rabin kudaden shigarta da kuma kusan kashi 90% na kudin waje.

Sai dai yawan man da ake hakowa ya ragu a shekarun baya-bayan nan, inda satar man da zagon kasa da kuma ficewar manyan kamfanoni daga wuraren da ake haƙo man saboda matsalar rashin tsaro, inda suke mayar da hankali kan binciken mai a teku.

Edun bai fayyace lokacin aiwatar da shirin bunƙasa tattalin arzikin ba.

People are also reading