Home Back

Uwargidan Mataimakin Gwamnan Niger, Hajiya Zainab Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

legit.ng 2 days ago
  • Rahotanni sun bayyana cewa Allah ya karɓi rayuwar uwargidan mataimakin gwamnan jihar Niger, Hajiya Zainab Garba
  • Gwamnan jihar Niger, Alhaji Mohammed Umaru Bago ne ya sanar da hakan a yau Talata a cikin sakon ta'aziyyar da ya fitar
  • Mai girma Umar Bago ya kwarara addu'ar neman gafarar Allah ga mamaciyar da kuma haƙuri ga mataimakinsa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Niger - Allah ya yiwa uwargidan mataimakin gwamnan jihar Niger rasuwa. Gwamnan jihar, Mohammed Umaru Bago ne ya bayyana hakan a ranar Talata.

Manomin gwamnan, Mohammed Umaru Bago, ya miƙa ta'aziyyarsa tare da alhini kan rasuwar Hajiya Zainab Garba.

Allah ya yiwa uwargidan mataimakin gwamnan Niger rasuwa.
Uwargidan mataimakin gwamnan Niger ta rigamu gidan gaskiya. Hoto: Sadiq Abdullahi Kwatu Asali: Facebook

Sakon ta'aziyyar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mista Bologi Ibrahim, babban sakataren watsa labaran Gwamna Bago ya fitar a shafin gwamnatin jihar na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matar mataimakin gwamna ta rasu

Gwamnan ya yi wa Hajiya Zainab Garba fatan samun yafiya daga Allah kuma Ya bata Aljanna. Ya kuma yi addu'ar dangana ga mataimakinsa da kuma ɗaukacin jama'ar jihar Niger.

Kamar yadda Ibrahim ya wallafa:

"Manomin gwamnan ya kuma yi addu'ar yafiyar allah kan kura-kuran mamaciyar tare da bata Aljanna Firdausi.
"Ya kuma yi addu'ar Allah ya baiwa mataimakinsa da ɗaukacin jama'ar jihar Niger haƙuri."

Mutane sun yi alhinin rashin Hajiya Zainab

Da muka duba shafin Facebook, mun ci karo da sakonnin ta'aziyya da kwamishinoni, masu rike da mukami da kuma wasu daga al'ummar jihar Neja suka aikawa mataimakin gwamnan.

Hon. Abdullahi Adamu Mammagi, kwamishinan ma'aikatar ilimi ta jihar Niger ya aika sakon ta'aziyyar rasuwar matar mataimakin gwamnan, Hajiya Zainab Yakubu Garba.

Shi ma shugaban karamar hukumar Mokwa Hon Jibril Muregi ya mika sakon ta'aziyya ga Kwamared Yakubu Garba, mataimakin gwamnan Neja bisa rasuwar matar sa Hajiya Zainab.

Mahaifiyar tsohon gwamna ta rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa mahaifiyar tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff ta rigamu gidan gaskiya.

Asali: Legit.ng

People are also reading