Uwargidan Mataimakin Gwamnan Niger, Hajiya Zainab Ta Riga Mu Gidan Gaskiya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Niger - Allah ya yiwa uwargidan mataimakin gwamnan jihar Niger rasuwa. Gwamnan jihar, Mohammed Umaru Bago ne ya bayyana hakan a ranar Talata.
Manomin gwamnan, Mohammed Umaru Bago, ya miƙa ta'aziyyarsa tare da alhini kan rasuwar Hajiya Zainab Garba.
Sakon ta'aziyyar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mista Bologi Ibrahim, babban sakataren watsa labaran Gwamna Bago ya fitar a shafin gwamnatin jihar na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya yi wa Hajiya Zainab Garba fatan samun yafiya daga Allah kuma Ya bata Aljanna. Ya kuma yi addu'ar dangana ga mataimakinsa da kuma ɗaukacin jama'ar jihar Niger.
Kamar yadda Ibrahim ya wallafa:
"Manomin gwamnan ya kuma yi addu'ar yafiyar allah kan kura-kuran mamaciyar tare da bata Aljanna Firdausi.
"Ya kuma yi addu'ar Allah ya baiwa mataimakinsa da ɗaukacin jama'ar jihar Niger haƙuri."
Da muka duba shafin Facebook, mun ci karo da sakonnin ta'aziyya da kwamishinoni, masu rike da mukami da kuma wasu daga al'ummar jihar Neja suka aikawa mataimakin gwamnan.
Hon. Abdullahi Adamu Mammagi, kwamishinan ma'aikatar ilimi ta jihar Niger ya aika sakon ta'aziyyar rasuwar matar mataimakin gwamnan, Hajiya Zainab Yakubu Garba.
Shi ma shugaban karamar hukumar Mokwa Hon Jibril Muregi ya mika sakon ta'aziyya ga Kwamared Yakubu Garba, mataimakin gwamnan Neja bisa rasuwar matar sa Hajiya Zainab.
A wani labarin, mun ruwaito cewa mahaifiyar tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff ta rigamu gidan gaskiya.
Asali: Legit.ng