Home Back

Gwamnatin Tarayya Ta Nada Rahama Sadau Mukami, Ali Nuhu Ya Magantu

legit.ng 2024/5/3
  • Jarumar fina-finai daga Arewacin Najeriya, Rahama Sadau ta samu mukamin mamba a kwamitin shirin iDICE na gwamnatin tarayya
  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya kaddamar da shirin domin tallafawa masana'antar kirkire-kirkiren abubuwan zamani
  • Tuni Ali Nuhu, babban daraktan hukumar fina-finai ta Najeriya ya aika sakon taya murnar samun wannan mukami ga Sadau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta nada jarumar fina-finai Rahama Sadau a matsayin mamba a kwamitin gwamnati da ke kula da shirin saka hannun jari a fannin kirkire-kirkiren zamani (iDICE).

Gwamnati ta nada Rahama Sadau mukami a kwamitin iDICE
Ali Nuhu ya taya Rahama Sadau murnar samun mukami a gwamnatin Tinubu. Hoto: Rahama Sadau Asali: Facebook

Rahama Sadau ta samu mukami

Rahama Sadau ta raba labarin nadin da aka yi mata a shafinta na Twitter, wanda wani Imran Muhammad ya wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun bayyana cewa mataimakin shugaban kasa Kashim Ibrahim Shettima ne ya kaddamar da kwamitin a ranar Laraba a Abuja.

Shirin iDICE hadin guiwa ne tsakanin gwamnati da hukumomin duniya da suka hada da bankin masana'antu, bankin raya Afrika, hukumar raya Faransa, da bankin bunkasa Musulunci.

Rahama Sadau da kwamitin shirin iDICE

Aikin shirin shi ne zakulowa tare da tallafawa mutane ko kamfanonin da suke da wata fikira ta zamani musamman a bangaren sana'o'i.

A yayin kaddamar da shirin, Shettima ya ce majalisar zartarwar Najeriya ta amince a fitar da $617.7m domin gudanar da shirin a jihohi 36 na kasar ciki har da Abuja.

An nada Rahama Sadau, Mr. Olumide Soyombo, Mrs. Kadaria Ahmed, Mr. Musa Ali-Baba da wasu a matsayin 'yan kwamitin shirin na iDICE.

Ali Nuhu ya taya Rahama Sadau murna

Jim kadan bayan da aka sanar da wannan nadin, babban daraktan hukumar fina-finai ta Najeriya, Ali Nuhu ya taya Sadau murnar samun wannan mukami.

Da yake taya jarumar murna a shafinsa na Facebook, Ali Nuhu ya ce:

"Ina taya daya daga cikin mu murnar samun mukami a kwamitin gudanar da shirin iDICE (Investment in Digital and Creative Enterprise)."

Wannan nadin na Rahama Sadau na zuwa ne bayan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Ali Nuhu muƙamin shugaban hukumar fina-finai ta kasa.

A halin yanzu dai Nuhu da Sadau ne jarumai daga Arewa da suke da mukami a gwamnatin APC mai mulki a kasar.

Jarumai sun taya Ali Nuhu murna

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa jaruman Kannywood, da masu shirya fina-finai har ma da 'yan bayan fage, sun taya Ali Nuhu murnar samun mukami.

Shugaban kasa Bola Tinubu ne ya nada Ali Nuhu mukamin shugaban hukumar fina-finai ta Najeriya.

Asali: Legit.ng

People are also reading