Home Back

'Yan Nijar sun koka da karancin abincin gwamnati

rfi.fr 2024/5/17

Domin rage wa jama'ar kasar Niger radadin tsadar rayuwar da suke fama da ita a irin wannan lokaci na azumi, gwamnatin mulkin sojin kasar ta kaddamar shirin da sayar da abinci a farashin mai rahusa a daukacin kasar.

Wallafawa ranar: 27/03/2024 - 18:17

Wata mata tare da yaranta a kauyen Tamou dake wajen birnin Yamai a Jamhuriyar Nijar.
Wata mata tare da yaranta a kauyen Tamou dake wajen birnin Yamai a Jamhuriyar Nijar. ASSOCIATED PRESS - TAGAZA DJIBO

Matakin dai ya karya farashin hatsi kan dala 80 maimakon 180 na kwano.

Karya farashin abincin ya sa magidanta na ta tururuwar zuwa kasuwannin da aka ware na musamman, amma saboda karamcin abincin ya sa ba kowa ke samu ba.

Magidanta da dama da masu unguwanni sun koka kan wannan al'amari saboda yawan mabukata da yanda ake kawo abun da bai taka kara ya karya ba.

Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken rahoton.

People are also reading