Home Back

Raba wa talakawa tallafi ƙasƙanci ne, ba ya magance raɗaɗin tsadar rayuwa – Gwamnan Bayelsa

premiumtimesng.com 2024/5/17
ZAƁEN GWAMNAN BAYELSA: Gwamna Diri ya jinjina wa INEC, ya nuna damuwa kan yankin Nembe

Gwamna Duoye Diri na Jihar Bayelsa, ya bayyana cewa raba wa talakawa da marasa galihu kayan tallafin abinci, ba shi ne hanyar magance raɗaɗin tsadar rayuwar da ake fama da ita ba.

Diri ya bayyana haka a ranar Lahadi, lokacin da yake jawabi Cocin St. Peter’s na Mabiya Ɗariƙar Angalika, a ƙauyen su mai suna Sampou da ke cikin Ƙaramar Hukumar Kolokuma/Opokuma.

Gwamna Diri ya ce duk da dai ba wai ba ya sukar raba kayan abincin tallafin ga mabuƙata, amma dai ya ce shi ya fi son a maida hankali wajen bijiro da tsare-tsare da shirye-shiryen da za a kafa talakawa bisa turbar magance raɗaɗin tsadar rayuwar da ake fama da ita a faɗin Najeriya.

Ya ce gwamnatin sa ta bijiro da tsare-tsaren da ta za su yi tasiri mai nisan zangon ga jama’a, maimakon tallafin kayan abincin da idan ka ci yau, ka ci gobe, to ya ƙare.

Ya ce gwamnatin sa na ci gaba da magance matsalar ma’aikata kuma ta na kakkafa makarantun fasaha a faɗin ƙananan hukumomi takwas da jihar Bayelsa ke da su.

Ya ce kuma ana ci gaba da gina titina waɗanda za su sauƙaƙa zirga-zirgar sufuri, ta yadda harkokin kasuwanci da bunƙasa tattalin arziki za su gudana cikin sauƙi.

Ya ce kuma ana gudanar da ayyukan koyar da sana’o’in hannu daban-daban.

Gwamnan ya ce gwamnati fa ba ta iya ƙosar da kowa, don haka sai ya yi kira ga kowa ya tashi ya kama sana’ar dogaro da kai domin ƙara wa kan sa nauyin aljihu, kuma a ƙara ciyar da jihar Bayelsa gaba.

People are also reading