Home Back

Al Maktoum: Dubai Za Ta Gina Tashar Jirgin Sama Mafi Girma a Duniya

legit.ng 2024/5/19
  • Domin zama lamba daya a harkar sufurin jiragen sama a duniya, Dubai za ta gina sabuwar tashar jiragen sama ta Al Maktoum
  • Idan aka kammala ginin, filin jiragen sama na Al Maktoum zai zama mafi girma a duniya kuma mafi tsada wajen ginawa
  • Mai mulkin ƙasar Dubai, Sheikh Mohammed bin Rashid al-Maktoum ya amince da kashe AED biliyan 128 (N43trn) wajen gina tashar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

UAE, Dubai - Mai mulkin ƙasar Dubai, Sheikh Mohammed bin Rashid al-Maktoum ya amince da gina sabuwar tashar fasinjoji a filin jiragen sama na Al Maktoum.

Dubai za ta gina tashar jirgin saman Al Maktoum mafi girma a duniya
Dubai za ta kashe Naira tiriliyan 43 domin gina sabuwar tashar jirgin saman Al Maktoum. Hoto: @HHShkMohd Asali: Twitter

Filin jirgi mafi girma a duniya

Kamar yadda ya sanar a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, Sheikh Rashid al-Maktoum, ya ce tashar za ta lakume AED biliyan 128 (N43trn).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Filin jiragen sama na Al Maktoum zai zama mafi girma a duniya yayin da zai iya daukar fasinja sama da miliyan 260 a lokaci daya.

Mai mulkin ƙasar ya ce filin jirgin Al Maktoum zai nunka girman filin jirgin Dubai sau biyar, wanda zai sa a mayar da ayyukan filin zuwa Al Maktoum a shekaru masu zuwa.

Dubai za ta zama lamba daya?

An ruwaito cewa za a samar da kofofin shiga tashar jirgi guda 400 a cikin filin jirgin Al Maktoum yayin da za a gina hanyoyin jirgi guda biyar.

Wannan sabon filin jiragen zai kasance gida ga kamfanin jiragen Emirates na kasar Dubai da takwararsa ta Flydubai da sauran jiragen da ke jigila a Dubai.

Sheikh Rashid al-Maktoum, ya ce wannan matakin zai jaddada matsayin Dubai na zama lamba daya a harkar sufurin jiragen sama a duniya.

Matakin farko na gina tashar jirgin

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Sheikh Ahmed bin Saeed Al Maktoum, shugaban kamfanin Emirates ya ce:

"Za a fara kashi na farko na aikin da kammala shi a cikin shekara 10, inda za a iya fara jigilar akalla fasinjoji miliyan 150 a lokaci daya."

Mahukunta na so tashar jirgin Al Maktoum idan an kammala ta maye gurbin tashar jirgin Dubai wacce ke jigilar fasinja miliyan 120 a shekara.

Me ya jawo ambaliyar ruwa a Dubai?

A wani rahoton, Legit Hausa ta yi nazari kan ikirarin ma'abota amfani da shafukan sada zumunta na cewa amfani da fasahar 'cloud seeding' ne ya jawo ambaliyar ruwa a Dubai.

Duk da cewa fasahar kirkirar gajimare kan iya zubar da ruwa mai yawan da zai iya jawo ambaliya, sai dai bincike ya nuna babu alakar ambaliyar ruwa a Dubai da fasahar 'cloud seeding.'

Asali: Legit.ng

People are also reading