Home Back

DPO’s ɗin mu duk wanda ya zo belin ƴan Daba ku riƙeshi – Kwamishinan ƴan sandan Kano.

dalafmkano.com 2024/5/17

Rundunar ƴan sandan Kano ta ce ta samar da rundunar yaƙi da ƴan Daba da ƴan Fashi da makamai, da suke addabar mutane a unguwar Ɗorayi ƙarama, tare da samar da gwangwanin Barkonon tsohuwa guda dubu ɗaya dan fara kakkaɓe ƴan Daba a yankin.

Kwamishinan ƴan sandan jihar CP Muhammad Usaini Gumel, ne ya bayyana hakan yayin wani taro na musamman da suka gudanar da masu ruwa da tsaki na unguwar Ɗorayi, da ya gudana yau a yankin wanda Kwamishinan ya jagoranta, domin lalubo hanyoyin magance matsalar tsaro a yankin.

CP Gumel, ya kuma umarci baturan ƴan sanda a faɗin jihar Kano, da su riƙe duk wanda yazo karɓar belin ƴan fashi da makamin da ta kama, kamar yadda wakilinmu Abba Isah Muhammad ya rawaito.

A ƴan tsakanin nan ne dai wasu rukunin matasa suka addabi al’ummar yankin na Ɗorayi, inda aka zargi sun yi kan mai uwa dawabi akan mutane da sara, tare da ƙwacen wayoyin al’umma, bayyana da aka ce sun rarraba takardu kan cewar za su kai harin tare da hana yin sallar Tarawi.

People are also reading