'Yan Kwadago Sun Ayyana Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani Kan Abubuwa 2 a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Kungiyoyin kwadagon Najeriya sun ayyana shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a fadin kasar nan daga ranar Litinin 3 ga watan Yuni, 2024.
Ƴan kwadagon sun ɗauki matakin tsunduma yajin aiki ne kan gazawar gwamnatin tarayya na ƙarƙare batun mafi karancin albashi da ƙara kuɗin wutar lantarki.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa tun da farko manyan kungiyoyin kwadagon ƙasar nan NLC da TUC sun nun alamun fara yajin aiki daga farkon makon gobe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƙungiyoyin sun nuna cewa matuƙar kwamitin mafi ƙarancin albashin da gwamnati ta kafa ya gaza amincewa da buƙatun ƴan kwadago, to tabbas za su shiga yaji.
A taron manema labarai, shugaban NLC da takwaransa na TUC, sun roki ‘yan Nijeriya da su jure duk halin da za a shiga.
Sun kuma bai wa mutane haƙuri da cewa, “Muna baku haƙuri kan duk abin da bai maku daɗi ba amma za mu yi haka ne domin kawo ƙarshen lamarin."
Ƙarin bayani na nan tafe...
Asali: Legit.ng