Home Back

Mun kama matashin da ake zargi da yiwa wani Matashi yankan Rago ya rasu a sabon titin Panshekara – Ƴan Sandan Kano

dalafmkano.com 2024/5/17

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta samu nasarar kama wani matashi mai suna Abba Garba, wanda akafi sani da Abba Ɗan Ƙuda, ɗan unguwar Ɗorayi Chiranchi, bisa zargin sa da kashe wani matashi mai suna Zaharaddin Ilyasu, ta hanyar yi masa yankan Rago a wuya, lamarin da ya ce ga garinku nan a daren jiya.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana wa gidan rediyon Dala FM, kama matashin a daren Asabar ɗin nan.

SP Kiyawa, ya ce jami’an su sun cafke Abba Ɗan Ƙuda, a lokacin da yake yinƙurin guduwa ƙasar Nijar, bayan da ya kashe matashin da wuƙar zarto, inda ya yanka wuyan sa bisa samun wani saɓani a tsakanin su.

Rahotanni sun bayyana cewar Ɗan Ƙuda, ya ƙaddamar wa marigayi Zaharaddini, (Zara) ne jiya Juma’a, bayan ƙarfe goma na dare, a sabon titin Panshekara, kan titin ring road, daura da gidan Kifi, bayan da suka je da wasu abokansa a cikin baburin Adai-dai Sahu, riƙe da muggan makamai, kamar yadda wani ɗan kasuwa a sabon titin ya shaida wa tashar Dala FM Kano.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da wasu ɓata garin matasa suka addabi al’ummar Ɗorayi, da Chiranchi, zuwa Sabon titin Panshekara, lamarin da rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta tashi haiƙan dan magance matsalar tsaro a yankin.

People are also reading