Home Back

Majalisa Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Dawo Da Wutar Lantarki A Arewa Maso Gabas

leadership.ng 2024/6/26
Matsanancin Rashin Lantarki Ya Addabi ‘Yan Nijeriya

Majalisar Dattawa ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta mayar da wutar lantarki a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya.  

Yankin dai ya shafe tsawon lokaci babu wutar lantarki sakamakon lalacewar manyan wayoyi.

Sanata Manu Haruna (Taraba ta Tsakiya) ne, ya bukaci a gyara layin wutar lantarki mai karfin 330KV da ke Jos zuwa Gombe.

Majalisar ta jaddada bukatar samar da kudade don gyara abubuwan da suka lalace tare da maido da wutar lantarki a yankin.

Sanata Kaka Lawan (Borno ta Tsakiya) da kuma Shaibu Lau (Taraba ta Arewa) sun bayyana rashin wutar a matsayin babbar damuwa.

Sun yi nuni da cewa wasu yankunan sun shafe shekaru biyu babu wutar lantarki amma sun dora alhakin hakan kan rashin kammala aikin wutar lantarki na Mambila.

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan (Yobe ta Arewa) ya tattauna batun rashin wutar lantarkin a majalisar.

Ya nuna damuwa da rahoton Majalisar Dinkin Duniya da ya bayyana yankin a matsayin mafi talauci a Nijeriya tare da jaddada bukatar samar da ababen more rayuwa.

Sanata Ahmed Wadada (Nasarawa ta Yamma) ya jajanta wa al’ummar Arewa maso Gabas, inda ya jaddada muhimmancin wutar lantarki ga rayuwarsu.

Ya bukaci shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da ya yi amfani da kujerarsa wajen inganta harkar wutar lantarki a yankin.

Majalisar ta kada kuri’a kan hanzarta aikin wutar lantarki na Makurdi zuwa Jalingo mai karfin 330KVA tare da aiwatar da dokar samar da wutar lantarki ta 2023.

People are also reading