Home Back

Hargitsi Ya Tashi a Majalisar Wakilai, Ana Zargin Mataimakin Kakaki da Nuna Bambanci

legit.ng 3 days ago
  • Wani lamarin mai kama da rikici ya ɓarke tsakanin mataimakin kakakin majalisar wakilai da wani ɗan majalisa, Hon. Cyril Hart
  • Cyril Hart ya zargi Kanu da ware duk sabbin zuwa majalisar a duk lokacin da ake muhawara idan shi ke shugabanta
  • Kalu ya musanta hakan amma Hart ya fusata tare da neman a basu dama suma, lamarin da ya kai ga ya fice daga zaman

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

FCT, Abuja - A ranar talata ne ɗan majalisar wakilai, Cyril Hart ya zargi mataimakin kakakin majalisar, Ben Kalu, da ware sabbin zuwa majalisar yayin tattaunawa a zauren.

Hon. Cyril, wanda zuwansa na farko kenan a majalisar daga mazaɓar Bonny/Degema a jihar Ribas, ya yi wannan zargin ne yayin muhawar harin bam da ya faru a jihar Borno.

Dan majalisar wakilai ya tayar da kura a zauren majalisa
Dan majalisar wakilai ya zargi kakakin majalisar da nuna bambanci. Hoto: @HouseNGR Asali: Facebook

Majalisar wakilai ta tattauna harin Borno

Ɗan majalisa Ahmad Jaha daga jam'iyyar APC ne ya miƙa buƙatar tattaunawar kan ƙunar baƙin waken, Premium Times ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin muhawarar, Kalu ya ba da dama ga tsohon mataimakin kakakin majalisa, Idris Wase, shugaban kwamitin sojin ruwa, Yusuf Gagdi, da shugaban kwamitin tsaro, Babajimi Benson, da su bada gudumawarsu.

Duk da mambobi masu yawa sun nuna son yin magana kan lamarin, Hon. Kalu yace ba zai bari a cigaba da tattauna maganar ba saboda babu lokaci.

Ana zargin Hon. Kalu da nuna bambanci

Jaridar Punch ta ruwaito cewa yayin da mataimakin kakakin majalisar yake ƙoƙarin bada damar yin ƙuri'a kan batun, Hon. Hart ya dakatar da hakan a fusace.

Hon. Hart ya zargi mataimakin kakakin majalisar da ware sababbin mambobi, inda ya ce manyan 'yan majalisar kaɗai ya bai wa damar magana kan lamarin.

Ya yi iƙirarin cewa, ya zama ɗabi'ar Kalu a koda yaushe yayin da yake shugabantar zama ya bada fifiko ga manyan 'yan majalisar.

"Ba ka ba da fifiko ga 'yan zuwan farko... ba ka bayarwa. Hakan kake yi kodayaushe. Akwai buƙatar ka baiwa sababbin zuwa damar yin magana."

- Yace.

Hon. Cyril ya fice daga zaman majalisar

Sai dai mataimakin kakakin majalisar bai yi gum da bakinsa kan wannan zargi ba, inda ya kare kansa da cewa:

"Babu banbanci a wannan majalisar."

Cike da rashin gamsuwa da kalaman Hon. Kalu, dan majalisar na Ribas ya cigaba da jawabi duk da kashe makirfo ɗinsa da aka yi, daga bisani kuma ya fice daga zauren majalisar.

Majalisa ta dauki mataki kan harin Borno

A wani labari na daban, mun ruwaito cewa ɗan majalisa mai wakiltar Damboa/Gwoza/Chibok a majalisar wakilai, ya ce sakacin jama'a da jami'an tsaro ne ya jawo harin bam a Borno.

A yayin da ya gabatar da kudurin gaggawa kan harin kunar bakin waken da aka kai yankin Gwoza, dan majalisar ya nemi da a gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin.

Asali: Legit.ng

People are also reading