Home Back

'Yan Kwadago: Shugaba Tinubu Ya Dauki Matakin Gaggawa Domin Hana Yajin Aiki

legit.ng 2024/6/26
  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dauki matakin gaggawa kan mafi ƙarancin albashin ma'aikata a Najeriya
  • Tinubu ya ba ministan kudi, Wale Edun umurnin tattaro da gabatar da sabon tsarin mafi ƙarancin albashi da gaggawa
  • Umurnin ya zo ne jim kaɗan bayan kungiyoyin NLC da TUC sun janye yajin aiki na mako guda domin cigaba ta tattaunawa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Biyo bayan janye yajin aikin 'yan kwadago na mako daya, shugaban kasa Bola Tinubu ya ba da umurnin gaggawa.

Bola Tinubu ya ba ministan kudi, Wale Edun umurni samar da tsarin biyan mafi ƙarancin albashi da zai dace da yanayin Najeriya.

Shugaba Tinubu
Bola Tinubu ya dauki matakin gaggawa kan karin albashi. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ministan yada labarai, Idris Muhammad ne ya bayyana haka a yammacin ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Umurnin Bola Tinubu kan karancin albashi

Shugaban kasa Bola Tinubu ya ba ministan kudi umurnin samar da sabon mafi ƙarancin albashi cikin sa'o'i 48, rahoton Tribune.

Ministan yada labarai, Idris Muhammad ya bayyana haka bayan kammala taro yau a fadar shugaban kasa.

Karin albashi: Mai zai faru bayan sa'o'i 48?

Bayan ministan kudi ya fitar da sabon mafi ƙarancin albashi, kwamitin da suke zama kan karin albashi za su zauna domin tabbatar da shi cikin mako daya.

'Yan kwamitin sun hada da kungiyoyin kwadago, kungiyoyin ma'aikata masu zaman kansu da jami'an gwamnatin tarayya.

Kokarin gwamnatin Tinubu kan karin albashi

Ministan yada labarai ya ce shugaban kasar ya yi kokari sosai wajen ganin an samu daidaito kuma yana shirye ya tabbatar da walwalar 'yan Najeriya.

Har ila yau ministan ya ce gwamnati ba kishiya ba ce ga kungiyoyin kwadago a kan samar da mafi ƙarancin albashi sai dai kawai suna aiki tare ne domin samar da cigaba a kasa baki daya.

Kungiyar NLC ta bukaci karin albashi

A wani rahoton, kun ji cewa yayin da ake cikin matsin tattalin arziki, kungiyar NLC ta bukaci N794, 000 a matsayin mafi karancin albashi.

Kungiyar ta bukaci hakan a wani taron ma'aikatan yankin Kudu maso Yamma, inda Shugaba Bola Tinubu ya fito, domin saukakawa ma'aikata rayuwa.

Asali: Legit.ng

People are also reading