Home Back

Shettima Ya Sa Labule da Gwamnoni Kan Sabon Mafi Ƙarancin Albashi da Wasu Batutuwa

legit.ng 2024/7/5

Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, gwamnonin jihohi da wasu mambobin majalisar tattalin arziki (NEC) sun shiga taro yanzu haka a Aso Villa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wannan taro na majalisar tattalin arziki na zuwa ne kwanki ƙalilan bayan majalisar zartaswa ta ɗage tattaunawa kan batun mafi ƙarancin albaahi.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.
Kashim Shettima na jagorantar taron NEC a fadar shugaban kasa Hoto: Kashim Shettima Asali: Facebook

Ministan yada labarau, Muhammad Idris, ya ce jingine batun ya zama wajibi domin shugaba Tinubu ya kara tuntubar sauran masu ruwa da tsaki kan lamarin.

Ana sa ran NEC za ta tattauna kan batun ƙarin albashin kuma mai yiwiwa ta cimma matsaya da ɗaukar mataki na gaba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A daren jiya ma kungiyar gwamnonin Nsjeeiya suka yi taro a Abuja inda suka tattauna kan sabon mafi karancin albashi da wasu batutuwan da suka shafi ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar bayan taron ta ce Gwamnonin sun amince da, "ci gaba da tuntuɓar masu ruwa da tsaki don cimma matsayar da ta dace."

Mambobin majalisar tattalin arazikin sun hada da gwamnonin jihohi 36, da gwamnan babban bankin kasa (CBN) da sauran waɗanda aka naɗa.

Mataimakin shugaban kasa ne ke jagorantar majalisar kuma suna taro kowane wata don bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tattalin arziki.

Gwamnonin da suka halarci taron karo na 141 da ke gudana yanzu haka sun haɗa da Usman Ododo (Kogi), Uba Sani (Kaduna), Lawal Dauda (Zamfara), da Charles Soludo (Anambra).

Sauran sun kunshi Seyi Makinde, (Oyo), Lucky Ayedatiwa, (Ondo) Abdullahi Sule, (Nasarawa), AbdulRahman AbdulRazaq (Kwara), Caleb Mutfwang, (Plateau), Hope Uzodimma (Imo) da Biodun Oyebanji (Ekiti).

Har ila yau Muhammed Inuwa Yahaya, (Gombe), Peter Mbah, (Enugu), Francis Nwifuru (Ebonyi), Dapo Abiodun, (Ogun), Umar Radda, (Katsina), Abba Yusuf (Kano), Umar Namadi, (Jigawa) da Umar Bago, (Niger) sun halarci taron.

Asali: Legit.ng

People are also reading