Home Back

Ƙungiyar Yarbawa Ta Buƙaci Gwamnati Da Ƙungiyar Ƙwadago Kan Lalubo Nagartaccen Mafi Ƙararancin Albashi

leadership.ng 2024/10/6
Ƙungiyar Yarbawa Ta Buƙaci Gwamnati Da Ƙungiyar Ƙwadago Kan Lalubo Nagartaccen Mafi Ƙararancin Albashi

Wata Kungiyar Yarbawa (YLT) ta bukaci gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago da su fito da sabon mafi karancin albashi nagartacce wanda ba zai kawo cikas ga makomar ‘yan Nijeriya ba.

Kungiyar wacce ta yabawa bangarorin biyu kan yadda suka tafiyar da tattaunawar mafi karancin albashi cikin taka tsantsan da kishin kasa ta ce, abin farin ciki ne yadda aka yi la’akari da maslahar ‘yan Nijeriya gaba daya a yayin tattaunawar.

Shugaban kungiyar, Alhaji Tajudeen Olusi ya yi kira ga dukkan bangarorin da ke kan teburin tattaunawa da su yi la’akari da makomar miliyoyin ‘yan Nijeriya da ba za su ci gajiyar karin mafi karancin albashi ba kai tsaye amma za su yi rayuwa tare da wadanda suka ci gajiyar tsarin komai tsanani.

People are also reading