Home Back

Zan Daga Darajar Wasanni A Kebbi – Gwamna Nasir Idris

leadership.ng 2024/5/12
Zan Daga Darajar Wasanni A Kebbi – Gwamna Nasir Idris

Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris ya jaddada aniyar gwamnatinsa na daga darajar wasanni a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a wajen bikin rufe gasar cin kofin matasa ta yankin yan majalisar dokokin jihar da aka gudanar a karamin filin wasa na FIFA da ke Birnin Kebbi.

Ya kuma bayar da tabbacin shirin gwamnatinsa na bunkasa harkokin wasanni a fadin jihar da nufin karfafa gwiwar matasa wajen nuna basirarsu.

Gwamnan ya kuma yi alkawarin kara inganta filayen wasanni da ke gundumomi a jihar da kuma bai wa ‘yan wasa maza da mata kwarin gwiwar shiga gasa a ciki da wajen jihar.

“,Na ji dadin abin da na gani kuma In Shaa Allahu gwamnatina za ta aiwatar da manufofin gaskiya da adalci ga matasa don kara samun nasara a fagen wasanni,” in ji shi.

Tun da farko an shirya gasar da nufin samar da hadin kai da kyakkyawar alaka a tsakanin matasan jihar.

Wasan karshen dai ya gudana ne tsakanin mazabar Birnin Kebbi/Kalgo/Bunza da kuma mazabar tarayya ta Augie/Arugungu inda ta kai matakin bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Mazabar Birnin Kebbi/Kalgo/Bunza ta lashe kofin kuma ta samu kyautar kudi Naira 500,000 daga hannun gwamnan.

Tags: Kebbi

People are also reading