Home Back

Amurka Na Yada Tsoro Domin Cimma Manufofin Babakere Da Fadada Moriya Kashin Kai

leadership.ng 5 days ago
Amurka Na Yada Tsoro Domin Cimma Manufofin Babakere Da Fadada Moriya Kashin Kai

A shekarar nan ta bana kasafin kudin kungiyar tsaro ta NATO ya kara hauhawa, inda kudaden kashewa a sassan Turai da Canada karkashin bukatar tsaro suka karu da kusan kaso 18 bisa dari, wanda shi ne kari mafi yawa da aka gani cikin gwamman shekaru a fannin, kamar dai yadda mahukuntan NATOn suka tabbatar.

Masharhanta da dama na cewa, mafi yawan wadannan kudade za a kashe su ne a Amurka, bayan da kasashe dake kawance da Amurkan a kungiyar su 23 suka shigar da a kalla kaso 2 bisa dari na GDPn su a harkar ta tsaro karkashin kungiyar a bana.

To sai dai kuma a daya bangaren, masu fashin baki na ganin amincewa da kashe karin kudade a fannin tsaro karkashin kungiyar NATO, ya biyo bayan yadda Amurka ke ta yada bayanai ne masu haifar da firgici, da tsoro tsakanin kawayen nata, musamman domin ta cimma ribar tattalin arziki daga hakan.

Alal misali, yayin barkewar rikicin Ukraine, Amurka ta yi ta yada farfaganda game da tsaron kasashe abokan kawancenta dake Turai, wanda hakan ya sanya su shiga shirin ko ta kwana a fannin ayyukan soji.

Hakan ya yi matukar amfanar masana’antun samar da hajojin ayyukan soji na Amurka, inda kasashen Turai kawayenta ke ta gaggauta sanya hannu kan kwangilolin sayo makamai daga gare ta, wadanda darajarsu ta kai kusan dala biliyan 140.

Hakan ne ma ya sa babban sakataren NATO ya taba cewa, kungiyar NATO ta amfani sashen tsaro na Amurka, da masana’antun ta, da ma fannin samar da guraben ayyukan yin kasar.

Da yawa daga masana harkar tsaro na ganin ba wai yawan kashe kudade ne kadai ke samar da tsaro ba, kuma tsaro ba ya samuwa ta hanyar daukar matakan kashin kai, kasancewar hakan na iya baiwa sauran sassa damar su ma su daura damara irin ta su.

Don haka dai, ga su wadannan kasashen Turai kawayen Amurka, ya kamata su yi karatun ta nutsu, duba da cewa tattara kudaden su a fannin tsaro kadai, tare da yin watsi da muhimman bukatun al’ummun su, da ayyukan bunkasa tattalin arziki, ba abun da zai haifar sai rashin daidaito tsakanin al’ummun su, da sanyawa al’ummun su nuna rashin gamsuwa da su. Mai yiwuwa hakan ma ya kai ga jefa al’ummun su cikin mawuyacin halin rayuwa, da “Haihuwar da maras ido”.

People are also reading