Home Back

Tsohuwar Jarumar Kannywood Fati Slow Ta Rasu

leadership.ng 2024/6/26
Tsohuwar Jarumar Kannywood Fati Slow Ta Rasu

Allah Ya yi wa tsohuwar jarumar Kannywood, Fati Slow rasuwa.

Wannan na cikin wani sako da tsohuwar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa, Mansura Isah ta wallafa a shafinta na Instagram da safiyar ranar Talata.

Mansura ta wallafa cewar “Innalillahi wainna illahi raji’un, Allah Ya yi wa Fati Slow rasuwa.

“Allah Ya jikanta, Allah Ya yi mata rahama, ameen.”

Mansura ta ce tsohuwar jarumar ta rasu ne a wani gari Abasha da ke kusa da Sudan, kuma tuni aka yi jana’izarta a can.

A cewarta yanzu haka ana zaman makokinta a gidansu da ke Unguwa Uku a Jihar Kano.

Fati Slow a baya ta fice a harkar fim din Hausa kafin daga bisani ta yi batan-dabo.

Jarumar a shekarar da ta wuce ta sha tayar da kura a kafafen sada zumunta.

Tuni ‘yan masana’antar Kannywood da sauran al’ummar Musulmi suka shiga yi mata addu’ar samun rahama da Ubangiji.

People are also reading