Home Back

Rusa majalisar zartaswar yaki ta Isra'ila

dw.com 2024/6/26
Firaminista Ministerpräsident Netanjahu na Isra'ila
Firaminista Ministerpräsident Netanjahu na Isra'ila

Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila ya rusa majalisar zastaswar yaki ta kasar mai mambobi shida, abin da ake zato gani tun lokacin da mai ra'ayin gaba-dai gaba-dai Benny Gantz tsohon babban habsan sojan kasar, ya fice daga cikin majalisar wadda aka kafa bayan harin da mayakan Hamas suka kai Isra'ila a watan Oktoba na shekarar da ta gabata.

Yanzu ana sa ran Firaminista Netanyahu zai ci gaba da shawara da kalilan daga cikin ministocin gwamnatinsa kan yakin da ke faruwa a yankin Zirin Gaza tsakanin tsagerun mayakan Hamas da dakarun Isra'ila.

People are also reading