Home Back

Kakakin Ma’aikatar Tsaron Kasar Sin Ya amsa Tambayoyin ’Yan Jaridu Game Da Sayarwa Taiwan Makamai Da Amurka Ta Yi A Sabon Zagaye

leadership.ng 2024/7/3
Kakakin Ma’aikatar Tsaron Kasar Sin Ya amsa Tambayoyin ’Yan Jaridu Game Da Sayarwa Taiwan Makamai Da Amurka Ta Yi A Sabon Zagaye

Kwanan nan ne cibiyar hadin-gwiwa kan tsaron gida ta ma’aikatar tsaron kasar Amurka ta sanar da cewa, kasar ta amince da wasu shirye-shirye guda biyu na sayar wa yankin Taiwan makamai masu darajar dala miliyan 360.

Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron kasar Sin, Wu Qian, ya amsa tambayoyin ‘yan jaridu game da batun a yau Jumma’a, inda ya ce, ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba Amurka ta sayar wa yankin Taiwan makamai, da yunkurin amfani da kudaden al’ummar Taiwan don raya gamayyar aikin soja da masana’antunta, har ma da mayar da Taiwan tamkar wurin ajiyar makamai. Mahukuntan jam’iyyar Democratic Progressive Party sun dogara kan wasu kasashen waje domin yunkurin neman ware Taiwan daga cikin kasar Sin, amma komai yawan makaman da suka sayo, ba za su taimaka ga samun tsaro ba, akasin haka, zai kai ga rura wutar yaki a Taiwan ne, har ma a karshe Amurka za ta yi fatali da Taiwan.

Kakakin ya kuma ce, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta cika alkawarin da ta dauka a zahirance, wato ba ta goyon-bayan masu yunkurin balle Taiwan daga kasar Sin, da dakatar da duk wani yunkurinta na taimakawa raya karfin soja na Taiwan. Rundunar sojan ‘yantar da al’ummar kasar Sin, wato PLA, za ta ci gaba da inganta karfin sojojin kasar, domin murkushe duk wani yunkuri na balle Taiwan daga cikin kasar. (Murtala Zhang)

People are also reading