Home Back

EFCC za ta ƙara maka shi kotu bisa ɓullar wata sabuwar ragabza da gadangarƙama a CBN

premiumtimesng.com 2024/5/13
RA’AYIN PREMIUM TIMES:  A gaggauta ceto Najeriya daga hannun Emefiele, ɗan ragabza da gidoga

Hukumar EFCC ta sake maka tsohon Gwamnan CBN, Godwin Emefiele a kotu, tare da gabatar da sabbin tuhume-tuhumen da suka haɗa da salwantar wata Dala biliyan 2 a lokacin da ya ke Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN).

A wannan gurfanarwa, ana yi wa Emefiele caji 26 a Babbar Kotun Jihar Legas da ke Ikeja.

“Emefiele bai bi ƙa’idar cire kuɗaɗen ba, dalili kenan laifin da ya aikata ya kawo tawaya ga ‘yan Najeriya.”

EFCC ta ce Emefiele ya aikata ɓaranƙyanƙyamar tsakanin 2022 da 2023, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito a ranar Juma’a.

Waɗannan sabbin tuhume-tuhume da ake wa Emefiele, lauyan EFCC ne, Rotimi Oyedepo ya shigar da su. Oyedepo dai babban lauya ne mai muƙamin SAN.

Za a gurfanar da Emefiele a gaban Mai Shari’a na Babbar Kotun Legas, Rahman Oshodi, a ranar Litinin, 8 ga Afrilu.

Sauran sun haɗa da karɓar ‘na goro’, karɓar kyautuka daga ejan-ejan, karɓar kyautar kadarori ba bisa ƙa’ida ba. Sai kuma tattago makusantan sa, ya haɗa baki da su ka shirga taɓargaza.

Ita dai Hukumar EFCC, ta sake maka tsohon Gwamnan CBN, Godwin Emefiele a kotu, tare da gabatar da sabbin tuhume-tuhumen da suka haɗa da salwantar wata Dala biliyan 2 a lokacin da ya ke Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN).

A wannan gurfanarwa, ana yi wa Emefiele caji 26 a Babbar Kotun Jihar Legas da ke Ikeja.

People are also reading