Home Back

AC Milan ta dauki Fonseca sabon kociyanta

bbc.com 2024/8/21
AC Milan

Asalin hoton, Getty Images

Kungiyar AC Milan ta dauki Paulo Fonseca a matakin sabon kociyanta.

Dan kasar Portugal, mai shekara 51 ya horar da Lille ta Faransa a 2022-2024, ya saka hannu kan yarjejeniyar da za ta kare a karshen 2027 da mai buga Serie A.

Ya maye gurbin Stefano Pioli, wanda ya bar AC Milan bayan da suka amince kowa ya kama gabansa, wanda ya kai kungiyar mataki na hudu a teburin Serie A.

Haka shima Fonseca ya raba gari da Lille suna girmama juna, bayan da kungiyar ta kare a mataki na hudu a teburin Ligue 1, amma ya kasa samu gurbin shiga Champions League da za a buga a badi.

Lille ta yi rashin nasara a hannun Aston Villa a bugun fenariti a quarter-finals a Europa Conference League da aka karkare a karshen kakar bana.

Haka kuma Fonesca ya horar da Roma da Shakhtar Donetsk da kuma Porto.

Ya lashe Super Cup a Portugal a 2013 tare da Porto da daukar babban kofin gasar Ukraine da na kalu balen kasar karo uku a Shakhtar.

People are also reading