Home Back

Mahara Sun Dira Jihar Binuwai a Babur, An Shiga Fargaba Bayan Kashe Rayuka

legit.ng 2024/7/3
  • Wasu mahara a kan babura sun farmaki kauyen Gugur a karamar hukumar Katsina Ala da ke jihar Binuwai inda su ka kashe mutane shida da ba su ji ba ba su gani ba
  • Wakilin yankin a majalisar jiha, Jonathan Agbidye ya tabbatar da harin sai dai ya ce harin na ramuwar gayya ne, kuma yanzu kora ta lafa kowa ya ci gaba da ayyukansa
  • ;Dan majalisar ya shaidawa manema labarai cewa a watan Afrilu ne wasu daga 'yan ta'addan su ka shiga hannun mutanen kauyen, aka yi artabu har aka kashe biyu daga cikinsu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Benue- Wasu ‘yan bindiga da ake zargin mazauna Binuwai ne sun dira yankin Gugur da ke karamar hukumar Katsina-Ala tare da kashe mutane shida

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun shiga yankin a kan babura da misalin karfe 9:00 zuwa 10:00 na daren Talata inda su ka ci karensu babu babbaka.

Legit
Mahara sun kashe mutane 6 a Binuwai Hoto: Legit.ng Asali: Original

A wani labari da Punch News ta wallafa, ta ce dan majalisar jiha mai wakiltar yankin Jonathan Agbidye ya tabbatar da kisan mutane shida daga mazabarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Harin ramuwar gayya ne,” dan majalisa

'Dan majalisar jiha a Binuwai, Jonathan Agbidye ya bayyana harin da yan bindiga su ka kai yankin da ya ke wakilta na Gugur da cewa na ramuwar gayya ne, kamar yadda Legit.ng ta wallafa.

Ya shaida cewa mutanen yankin ba su goyon bayan ta’addanci, wanda haka ne ya sanya wani artabu da aka yi su ka kama miyagu biyu kuma su ka kashe su a watan Afrilu.

Jonathan Agbidye ya kara da cewa wancan mataki na al’umar yankin ne ya sanya yan ta’addan daukar fansa a daren Talata.

Gwamnati ta tabbatar da harin Binuwai

Shi ma shugaban karamar hukumar Katsina Ala, Shaku Justine ya tabbatar da afkuwar mummunan lamarin.

Amma rundunar ‘yan sandan jihar ta ce ba ta samu labarin harin ba zuwa lokacin.

Binuwai: Sojoji sun aika ‘yan ta’adda lahira

A wani labarin kuma kun ji cewa jami’an sojojin Najeriya sun yi galaba kan yan ta’adda bayan sun samu nasarar hallaka wasu daga cikinsu a samamen da su ka kai.

Jami’an sun kai farmaki maboyar yan bindiga a Sankara da ke karamar hukumar Ukum, inda su ka ceto wasu mutane biyu, haka kuma an kara ceto wasu daga karamar hukumar Gwer

Asali: Legit.ng

People are also reading