Home Back

Kasashen duniya sun caccaki Iran bayan harin Isra'ila

dw.com 2024/5/12
Hoto: White House/AFP

Kasashen duniya sun yi allawadai da harin da Iran ta kai wa Isra'ila, tare da yin gargadin cewa hakan ka iya dagula zaman lafiyar yankin Gabas ta Tsakiya.

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce ya gana da mashawarcinsa ta fuskar tsaro kan batun, kuma babu gudu babu ja da baya suna tare da Isra'ila. Shi kuwa firaministan Burtaniya Rishi Sunak cewa ya yi Iran ta kirawo wa kanta ruwa. Yayin da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya kira harin da rashin tunani.

Saudi Arebiya da Rasha da kuma Qatar sun yi kira ga bangarorin biyu da su mayar da wukakensu cikin kube, su rungumi zaman lafiya, har ma suka bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta shiga tsakani don kare al'ummar yankin daga fuskantar yaki.

Shi ma sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi tir da harin na Iran, tare da bayyana fargabarsa ga hatsarin yaki a nan gaba. Ita kuwa shugabar hukumar gudanarwar tarayyar Turai Ursula von der Leyen, jan hankalin Iran ta yi da ta gagauta dakatar da kai harin haka.

Kungiyar tsaro ta NATO ma ta yi nata allawadan, da nuna muhimmancin kaucewa fantsamar rikicin Gabas ta Tsakiya.

Iran ta yi sammacin Jakadun Burtaniya da Faransa da kuma Jamus, domin jin ta bakinsu kan cukumurdar da ke wakana tsakaninta da Israi'la, bayan sun soki lamirin harin ramuwar gayyar da ta kai wa Isra'ila.

Iran dai ta zargi kasashen uku da fuska biyu, bayan da suka ki amincewa da kudurin da Rasha ta gabatarwa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, da ya yi allawadai da harin da Isra'ila ta kai wa ofishin jakadancinta na Syria kwanakin baya.

Nan gaba a Lahadin nan ne dai kasashen G7 masu kasu karfin tattalin arziki na duniya za su yi taro na musamman don tattauna batun harin na Iran.

Kasashen su ne Amurka da Burtaniya da Jamus da Faransa, sai Italiya da Japan da kuma Canada.

Filayen jiragen saman Iran da dama ciki har da na Tehran babban birnin kasar, sun soke jigilar fasinjoji a Lahadin nan, sakamakon fargabar da ake fuskanta, biyo bayan harin da Iran din ta kai wa Isra'ila cikin daren Asabar.

Kafar yada labaran kasar ta rawaito hukumar kula da sufurin jiragen saman Iran na cewa sokewar ta shafi zirga-zirgar jiragen a cikin gida da kuma ketare.

Tuni dai wasu kamfanonin sufurin jiragen sama suka sanar da soke jigilarsu zuwa yankin Gabas ta Tsakiya, har ma suka karkata akalar jiragen zuwa wasu wurare.

Ciki har da Lufthsansa na nan Jamus, da ya dakatar da sufurinsa a Isra'ila da Jordan da Iran da Iraq da kuma Lebanon.

People are also reading