Home Back

Tuna Baya: Lokacin da Jonathan Ya Fusata Amurka da Sa Hannu a Dokar Haramta Auren Jinsi

legit.ng 2024/10/6
  • A lokacin yana shugaban kasa, Dr. Goodluck Jonathan ya amince da dokar haramta dangantakar jinsi a Najeriya
  • Shugaban Najeriyan ya jawo fushin kasashen yamma masu goyon bayan LGBT a dalilin wannan mataki da ya dauka
  • Gwamnatin Goodluck Jonathan ta yaki auren jinsi da kafa kungiyoyi ko gidajen da ake luwadi ko madigo a kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - A wata ranar 13 ga watan Junairu 2014, Dr. Goodluck Jonathan ya sa hannu a dokar da ta jawo maganganu iri-iri.

Shugaban Najeriya a lokacin, Dr. Goodluck Jonathan ya amince da kudirin da ta haramta aure da duk wata dangantakar jinsi.

The Guardian ta rahoto cewa Mai girma Goodluck Jonathan ya kawo dokar da ta laftawa luwadi da madigo daurin shekaru 14.

Dokar haramta alakar jinsi a Najeriya

Duk wanda aka samu ya auri jinsinsa ko dai wata alaka zai iya shafe shekaru 12 a daure.

Dokar ta haramta rajista ko kafa gidajen luwadi ko madigo ko kuwa a kirkiro wata kungiya da ke goyon bayan muradun LGBT a kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wanda aka samu ya na tallata wannan danyen aiki ko ya fito fili yana nuna alakarsa da jinsisa a fili, zai iya yin shekaru goma a daure.

Auren jinsi: Amurka ta kalubalanci Jonathan

Sakataren gwamnatin Amurka, Mista John Kerry ya yi tir da dokar, ya nun aba su goyon bayan matakin da Jonathan ya dauka.

Baya ga haramta aure ko wata alaka tsakanin maza ko mata, gwamnatin kasar Amurka ta ce dokar ta take hakkin Bil Adama.

A lokacin, an ji John Kerry ya yi ikirarin jama’a suna da hakkin sha’awar abin da suke so.

Reuters ta ce tun shekarar 2006 ake wannan yunkuri amma ba a iya cin ma nasara ba.

Mai girma Goodluck Jonathan ya rattaba hannu a kudirin, hakan yana nufin duk wanda aka samu da laifi zai shiga magarkama a Najeriya.

Asali: Legit.ng

People are also reading