Home Back

Akpabio ya yi kira ga Sufeto Janar, ya yi waje da gurɓatattun ƴan sanda

premiumtimesng.com 2024/5/17
Akpabio ya yi kira ga Sufeto Janar, ya yi waje da  gurɓatattun ƴan sanda

Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya yi kira ga Sufeto Janar ɗin ‘Yan Sanda Kayode Egbetokun ya cire baragurbin ma’aikata a rundunar.

Akpabio ya fadi haka ne a taron karrama fitattun ƴan sanda da rundunar ta yi ranar a Abuja.

Ya kuma kara yin kira ga rundunar da ta dauki tsauraran matakai domin kawo karshen cin hanci da rashawa tsakanin ‘yan sanda da mutane.

“Karuwar da ake samu na muggan aiyuka na jawo wa kasar nan matsaloli sannan yayin da muke girmama hafsoshi nagari, kamata ya yi a kawar da baragurbin ma’aikata domin inganta tsaro a kasan.

“Rundunar ‘yan sanda za ta bukaci goyan bayan mutane da masu ruwa da tsaki domin gamawa da cin hanci da rashawa a kasar nan.

Akpabio ya taya wadanda aka karrama murna sannan ya hore su da su ci gaba da aiki domin samar da ci gaba a kasar nan.

People are also reading