Home Back

Jam’iyyar Labour Ta Kwace Majalisar Ingila, Keir Starmer Ya Zama Sabon Firaminista

legit.ng 2024/8/21
  • Jam'iyyar Labour a Ingila ta yi nasarar samun kujeru mafin rinjaye a House of Commons, inda a yanzu za ta samar da firaminista
  • Keir Starmer, dan takara a jami'iyyar Labour shi ne za a rantsar matsayin sabon firaminista bayan fitar sakamakon zaben
  • Rishi Sunak, dan takarar firaminista na jam'iyyar Conservative, ya rungumin kayen da ya shatare da taya Keir Starmer murna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Burtaniya - Keir Starmer, dan takarar jam'iyyar dawa ta Labour, ya yi nasara a babban zaben Ingila kuma shi ne zai zama firaminista na gaba.

Jam'iyyar adawa ta Labour ta yi nasarar samun kujeru 326 na majalisar da ake bukata.

Ingila tayi sabon firayim minista. Hoto daga @Keir_Starmer
Ingila Tayi Sabon Firayim Minista, Sunak Ya Taya Shi Murnar Nasara a Zabe Asali: Twitter

Firaminista Rishi ya karbi kaddara

Firayim minista mai barin gado, Rishi Sunak, ya rungumi kayen da ya sha inda ya dauki alhakin faduwar jam'iyyarsa ta Conservative, in ji rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rishi Sunak ya bayyana godiyarsa ga jama'ar mazabarsa tare da taya Keir Starmer murna kan nasarar da ya samu.

Ya ce zai mika mulki cikin lumana tare da fatan alheri a kowanne bangare. Sunak ya baiwa sauran 'yan jam'iyyarsa da suka fadi hakuri.

Yadda zaben UK ya gudana

Rahoton BBC ya nuna cewa zuwa yanzu an bayyana kusan dukkanin sakamakon zaben, ana hasashen jam'iyyar Labour za ta kafa gwamnati mai zuwa, tare da mafi yawan 'yan majalisu.

An ruwaito kasar Ingila ta yi babban zabenta a ranar Alhamis, 4 ga watan Yuli inda miliyoyin jama'a suka kada kuri'ar zaben 'yan majalisa.

'Yan majalisar da aka zaba a yanzu, za su wakilci mazabunsu da mutanensu a babbar majalisar Ingilan ta House of Commons.

Yadda zauren majalisar ingila yake

Mazabun Ingila sun kasu har zuwa 650, inda kowacce maza ta zabi dan majalisa daya domin wakiltarta.

Yayin da yawancin 'yan takarar na wakiltar jam'iyyar siyasa, wasu kuma sun yi takara ne ba tare da jam'iyya ba.

Zaben yana da daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a jadawalin siyasar Ingila.

An ce zaben ya gyara akalar makomar siyasar kasar tare da bayyana shugabannin da zasu dinga yanke muhimman hukunci a madadin 'yan kasa.

'Yan kwangila 39 zasu fuskanci majalisa

A wani labari na daban, majalisar dattawan Najeriya ta fusata da wasu 'yan kwangila 39 da suka karba kudi suka ki fara aiki.

Ministan ayyuka, David Umahi, ya sanar da cewa zasu tuhumesu kuma su yi amfani da EFCC wurin karbo kudin gwamnati da suka mallake.

Asali: Legit.ng

People are also reading