Home Back

Kotu Ta Taso Tsohon Gwamnan CBN a Gaba, Ta Ƙwace Wasu Manyan Kadarori a Abuja

legit.ng 2024/7/2
  • Kotu ta bayar da umarnin kwace wasu manyan gidaje da kadarorin makudan kuɗi daga hannun tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele
  • Mai shari'a Chukwujekwu Aneke ya umarci gwamnatin tarayya ta karɓe kadarorin waɗanda galibi suke cikin birnin Abuja
  • Wannan na zuwa ne yayin da tsohon gwamnan CBN ke ci gaba da fuskantar shari'a kan zargin almundahana kala daban-daban

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Babbar kotun tarayya mai zama a Legas ta bayar da umarnin kwace gidaje da wasu kadarori da suka haura N11bn da ke da alaƙa da Mista Godwin Emefiele.

Kotun ta kwace waɗannan kadarorin na makudan kuɗaɗe daga hannun tsohon gwamnan babban banki CBN, ta miƙawa gwamnatin tarayya.

Godwin Emefiele.
Kotu ta amince da buƙatar kwace kadarorin Emefiele da duka haura N11bn Hoto: Mr Godwin Emefiele Asali: Facebook

Mai shari'a Chukwujekwu Aneke ne ya bada umarnin kwace kadarorin na dindindin bayan sauraron ƙorafi daga hukumar EFCC ta hannun lauyanta, Chineye Okezie.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Channels tv ta ruwaito cewa a ranar 5 ga watan Yuni, Alƙalin ya amince da buƙatar lauyan hukumar yaƙi da rashawa (EFCC) na kwace kadarorin na wucin gadi.

Lauyan EFCC Oyedepo ya shaidawa kotun cewa ana zargin Emefiele ya yi amfani da wakilai ya sayi waɗannan kadarorin da kuɗin baitul-malin da ya sata.

Ya bayyana sunayen ma'aikatan CBN guda biyu da wani mutum ɗaya da ya yi ritaya, waɗanda ake zargin sun haɗa baki da Emefiele wajen sayen kadarorin.

Galibin waɗannan gudaje da shaguna suna kewayen babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Yayin da aka dawo zaman shari'ar jiya Jumu'a, 21 ga watan Yuni, 2023 babu wanda ya zo ya ƙalubalanci umarnin kwace kadarorin na wucin gadi.

Daga nan kuma Chineye Okezie ta ƙara mika bukatar kwace su na har abada ga alkali.

Bayan karanta bayanan mai gudanar da bincike na EFCC, Alkalo Aneke ya amince da buƙatar kwace kadarorin na dindindin.

A wani rahoton na daban Babbar Kotun Tarayya ta yi fatali da korafin neman sallamar shugaban EFCC, Ola Olukoyede daga mukaminsa.

Wani lauya mai suna Victor Opatola shi ya ke kalubalantar nada Olukoyede a matsayin shugaban hukumar yaƙi da masu cin hanci da rashawa EFCC.

Asali: Legit.ng

People are also reading