Shugaban Majalisa Abin da 'Yan Najeriya Za Su Yi Bayan Tinubu Ya Gama Mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya yi kira ga ƴan Najeriya da su marawa shugaban ƙasa Bola Tinubu baya.
Godswill Akpabio ya yi wannan kiran ne domin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta yi nasara.
Shugaban majalisar dattawan ya buƙaci hakan ne yayin ƙaddamar da tashar mota ta Kugbo da ke Abuja, cewar rahoton tashar Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Godswill Akpabio ya ce da goyon bayan ƴan ƙasa, gwamnatin Tinubu za ta yi nasara.
"Ba ni da shakku kan cewa a lokacin da shugaban ƙasa ya cika wa’adin mulkinsa a ƙasar nan, shekara bakwai daga yau, mutane da dama ba za su gane birnin tarayya ba, ba za su sake gane Najeriya ba."
"Saboda haka abin da kawai zan ce shi ne mu ci gaba da yi masa addu'a tare da fatan cewa ƙalubalen da muke fuskanta a yanzu, nan gaba ba za mu fuskance su ba."
- Sanata Godswill Akpabio
A cewarsa ƙaddamar da aikin ya nuna yadda gwamnati ta himmatu wajen kyautata rayuwa da jin daɗin mazauna birnin tarayya Abuja.
Ya kuma yabawa Shugaba Tinubu bisa naɗa Nyesom Wike a matsayin ministan babban birnin tarayya Abuja.
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Akpabio ya bayyana cewa Tinubu yana ƙoƙarin gyara tattalin arziƙin ƙasar nan ne wanda ya zargi tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele, da yi masa babban giɓi.
Asali: Legit.ng