Home Back

Shugaban Majalisa Abin da 'Yan Najeriya Za Su Yi Bayan Tinubu Ya Gama Mulki

legit.ng 2 days ago
  • Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya buƙaci ƴan Najeriya da su sanya gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu a cikin addu'a
  • Godswill Akpabio wanda ya buƙaci ƴan Najeriya su marawa Tinubu baya, ya ce hakan zai sanya gwamnatinsa ta samu nasara a ƙasar nan
  • Ya kuma bayyana cewa mutane da dama ba za su sake gane Najeriya ba a lokacin da Tinubu zai kammala mulkinsa saboda ɗumbin ayyukan ci gaban da zai yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya yi kira ga ƴan Najeriya da su marawa shugaban ƙasa Bola Tinubu baya.

Godswill Akpabio ya yi wannan kiran ne domin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta yi nasara.

Akpabio ya bukaci 'yan Najeriya su yiwa Tinubu addu'a
Godswill Akpabio na son gwamnatin Tinubu ta yi nasara Hoto: @DOlusegun Asali: Twitter

Shugaban majalisar dattawan ya buƙaci hakan ne yayin ƙaddamar da tashar mota ta Kugbo da ke Abuja, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Akpabio ya ce kan gwamnatin Tinubu

Sanata Godswill Akpabio ya ce da goyon bayan ƴan ƙasa, gwamnatin Tinubu za ta yi nasara.

"Ba ni da shakku kan cewa a lokacin da shugaban ƙasa ya cika wa’adin mulkinsa a ƙasar nan, shekara bakwai daga yau, mutane da dama ba za su gane birnin tarayya ba, ba za su sake gane Najeriya ba."
"Saboda haka abin da kawai zan ce shi ne mu ci gaba da yi masa addu'a tare da fatan cewa ƙalubalen da muke fuskanta a yanzu, nan gaba ba za mu fuskance su ba."

- Sanata Godswill Akpabio

Akpabio ya yabawa gwamnatin Tinubu

A cewarsa ƙaddamar da aikin ya nuna yadda gwamnati ta himmatu wajen kyautata rayuwa da jin daɗin mazauna birnin tarayya Abuja.

Ya kuma yabawa Shugaba Tinubu bisa naɗa Nyesom Wike a matsayin ministan babban birnin tarayya Abuja.

Akpabio ya ba ƴan Najeriya haƙuri

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Akpabio ya bayyana cewa Tinubu yana ƙoƙarin gyara tattalin arziƙin ƙasar nan ne wanda ya zargi tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele, da yi masa babban giɓi.

Asali: Legit.ng

People are also reading