Home Back

Farfesa Aisha Maikudi Ta Zama Mukaddashiyar Shugaban Jami’ar Abuja

leadership.ng 3 days ago
Farfesa Aisha Maikudi Ta Zama Mukaddashiyar Shugaban Jami’ar Abuja

Bayan kammala wa’adin Farfesa AbdulRasheed Na’Allah, a matsayin Shugaban Jami’ar Abuja (UniAbuja), na 6 a ranar 30 ga Yunin 2024, hukumar gudanarwar Jami’ar ta zabi Farfesa Aisha Sani Maikudi a matsayin mukaddashiyar shugabar jam’iar har zuwa lokacin da za a nada sabon shugaban.

Ta kasance Farfesa a fannin shari’a ta kasa da kasa kuma mataimakiyar shugaban jami’a a fannin ilimi a yanzu.

Ta yi karatu a Jami’a a Ingila, inda ta samu digirinta na farko da na biyu a kan shari’a sannan ta halarci makarantar aikin lauya ta Nijeriya, da ke Abuja, kana ta wuce Jami’ar Abuja don neman digirin digirgir.

Maikudi ta fara aiki da Jami’ar Abuja, a matsayin malama kuma ta zama mace ta farko karamar shugabar Sashen Koyarwar Shari’a a 2014.

Har wa yau ta kasance mace ta farko da ta rike mataimakiyar shugaban tsangayar shari’a a 2018, da kuma mukamin babbar daraktan Jami’ar Abuja.

People are also reading