Home Back

Burkina Faso ta dakatar da shirye-shiryen BBC da VOA

dw.com 2024/5/7
Burkina Faso, Ouagadoudou | Ibrahim Traore
Hoto: Kilaye Bationo/AP/picture alliance

Labarin na HRW ya zargi sojojin kasar ne da kisan mutane babu gaira babu dalili kamar yadda hukumomi suka bayyana a daren Juma'a.

Rahoton binciken na kungiyar ya ce sojojin kasar ta yammacin Afirka sun kashe wasu mutanen karkara akalla 223 ciki har da kananan yara 56 a watan Fabrairu.

Kisan mutanen wani yunkuri ne na kakkabe fararaen hula da aka zarga da hada kai da masu tada kayar baya a cewar rahoton.

Hukumomin kasar ta Burkina Fasoa cikin wata sanarwa sun umurci kamfanonin sadarwar intanet su katse hanyoyin sadarwa ga shafukan intanet na BBC da kuma VOA da ma ita kanta kungiyar HRW.

People are also reading