Home Back

Kasar Philippines Na Kara Hauka Kan Batun Tekun Kudancin Kasar Sin

leadership.ng 2024/7/3
Kasar Philippines Na Kara Hauka Kan Batun Tekun Kudancin Kasar Sin

Kasar Philippines na kara tada fitina a yankin tekun kudancin kasar Sin. Bisa rahoton da hukumar ‘yan sandan ruwa ta kasar Sin ta bayar, a ranar 17 ga watan Yuni, kasar Philippines ta aike da wani jirgin ruwa dauke da kaya da wasu kwale kwalen tafi da gidanka guda biyu don shiga cikin yankin tekun da ke dab da karamin tsibirin Ren’ai na tsibiran Nansha na kasar Sin ba bisa ka’ida ba, da nufin jigilar kayayyaki zuwa jiragin ruwan yaki dake girke a can ba bisa doka ba. ‘Yan sandan ruwan kasar Sin sun dauki matakai kan jiragen ruwan Philippines bisa doka da kwarewa.

Idan aka waiwayi abin da kasar Philippines ta aikata kan batun tekun kudancin kasar Sin tun daga watan Mayun bana, ana iya gano cewa, bisa ingizawar Amurka, Philippines na kara hauka kan batun.

Tsibiran tekun kudancin kasar Sin sun kasance yankin dake karkashin ikon kasar Sin tun da dadewa. Kuma Kasar Sin tana da isasshen karfi bisa tushen doka don mayar da martani ga ayyukan keta ikonta da na tsokana daga kasashen waje. Game da batun tekun kudancin kasar Sin, matsayin da kasar ke dauka a ko da yaushe a bayyane yake, wato nacewa kan warware rikice-rikice da bambance-bambancen da ake da shi kan teku, ta hanyar yin shawarwari da tuntubar kasashen da abin ya shafa kai tsaye, da kuma mayar da martani ga duk wani aiki na cin zarafi da tsokana a yankin teku. Wannan ba wai kawai kariya ce ga hakkin tekun kasar Sin ba, har ma da goyon bayan zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. (Bilkisu Xin)

People are also reading