Kakakin Majalisa Ya Nemi Afuwa Bayan 'Yan Majalisu Sun Kusa Ba Hammata Iska
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Edo - Kakakin majalisar dokokin Edo, Blessing Agbebaku, ya ba da haƙuri kan hatsaniyar da aka samu a majalisar lokacin dakatar da wasu mambobin majalisar a ranar Litinin.
Blessing Agbebaku wanda ke jagorantar majalisar dokokin ya ba da haƙurin ne a ranar Talata, 7 ga watan Mayun 2024, cewar rahoton jaridar The Nation.
Kakakin majalisar a ranar Litinin, 6 ga watan Mayun 2024 ya dakatar da wasu ƴan majalisa uku bisa zarginsu da yunƙurin tsige shi da wasu shugabannin majalisar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan majalisar da aka dakatar sune Okogbe Donald Okogbe (PDP, Akoko-Edo II), Adheh Isibor (APC, Esan Arewa ta Gabas I), Iyamu Bright (PDP, Orhionnwon).
A kalamansa:
"Ina so na nemi afuwar mambobin wannan majalisa kan abin da ya faru a ranar Litinin a zaman majalisa. Ba nufinmu ba ne mu haifar da tashin hankali a cikin majalisa."
"Mun yi alkawarin hakan ba zai sake faruwa ba. Wannan haƙurin da muka ba da mun bayar ne saboda muna ganin girman ku."
Jaridar Leadership ta ce shugabancin jam’iyyar PDP a jihar ya sanya baki a rikicin da ya kai ga dakatar da ƴan majalisar domin a dawo da su.
Wasu daga cikin mambobin sun gana da kakakin majalisar na tsawon sa’o’i a ƙoƙarin ganin an shawo kan rikicin da kuma tabbatar da cewa ƴan majalisar da aka dakatar sun koma majalisar.
Ɗaya daga cikinsu wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce manufar taron ita ce a nemo hanyoyin da za a janye dakatarwar.
A kalamansa:
"Mun haɗu a ranar Talata domin nemo hanyar ɗage dakatarwar da aka yi wa mambobin uku. Za a yi taro a ranar Alhamis kuma da fatan za a ɗage dakatarwar ranar Litinin a zaman majalisa na ranar."
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dokokin jjar Edo ta tsige mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu, daga muƙaminsa bayan an kammala bincike.
Tsigewar ta biyo bayan amincewa da rahoton kwamitin bincike na mutum bakwai da majalisar ta kafa domin bincikar zarge-zargen da ake yi wa Shaibu.
Asali: Legit.ng