Home Back

CISLAC Ta Yi Taron Manema Labarai Kan Bikin Ranar Yaƙi Da Shan Taba Sigari Ta Duniya Ta 2024

leadership.ng 2024/7/1
CISLAC Ta Yi Taron Manema Labarai Kan Bikin Ranar Yaƙi Da Shan Taba Sigari Ta Duniya Ta 2024

“Ranar yaki da shan taba sigari ta duniya”, wani taro ne da ake gabatar da shi a duk ranar 31 ga watan Mayun kowacce shekara, wanda Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) ta kirkiro don nuna irin illar da barazanar da ke tattare da lafiya da tattalin arziki da zamantakewa ga masu shan taba sigari.

Duba da irin haɗarin da ke tattare da shan taba sigari, WHO ta himmatu wajen wayar da kai da bayar da shawara don rage sha da ta’ammali da taba sigari.

Manufar bikin shi ne yaki da shan taba sigari da mayar da hankali wajen wayar da kan jama’a game da hadarin da ke tattare da shan taba sigari da lalubo hanyoyi da dabarun kare kananan yara masu tasowa daga fadawa cikin masu shan taba sigari.

Taken bikin na wannan shekarar shi ne “Kare yara daga fadawa shan taba sigari” Wannan batu ne mai matukar muhimmanci da zai wayar da kan al’umma da janyo hankalin gwamnati da masu ruwa da tsaki don kare yara daga fadawa shan taba sigari ta hanyar wayar da kan jama’a da bayar da shawarwari kan illar da ke tattare da hakan.

A wani ɓangare na bikin farin ciki da yaki da shan taba sigari na bikin na 2024, yasa Cibiyar Rajin Kyautata Ayyukan Majalisun Dokoki da Yaƙi da Rashawa a Nijeriyar (CISLAC) a karkashin jagorancin shugabanta na Kasa a Nijeriaya, Auwal Ibrahim Musa (Rasfanjani) ta shirya taron manema labarai saboda irin muhimmiyar rawar da kafafen yada labarai za su taka wajen jawo hankulan jama’a kan bukatar kare ‘yan Nijeriya da yara masu tasowa daga illolin da ke tattare da shan taba sigari.

Taron wanda aka shirya shi a ranar Juma’a 31,ga watan Mayun 2024 a Otel din R & K da ke Kano.

People are also reading