Gimbiyoyin Kannywood (4)
Fatima Abdullahi Washa
Wani suna da ba zai taba goguwa a cikin littafin tarihin masana’antar Kannywood ba shi ne Fatima Abdullahi Washa wadda akafi sani da Fati Washa, sakamakon rawar da ta taka kuma take ci gaba da takawa a masana’antar, ganinta a cikin akwatin talabijin yana saka masoyanta jin dadi da annashuwa sakamakon baiwar da Allah ya bata ta iya kowane irin matsayi aka bata a cikin fim.
Jarumar wadda ta fara harkar fim a shekarar 2015 ta zamo daya daga cikin manyan jarumai mata da suka samu kyautar gwarzuwar jarumar Kannywood wadda kungiyar City People Mobie Award take bayarwa a shekarar 2015 sakamakon rawar da ta taka a manyan fina-finanta da suka hada da Kalan Dangi, Jaraba da kuma Rariya inda ta fito a mataimakiyar babbar jaruma.
Zainab Abdullahi (Indomie)
Manyan fina-finan da jarumar ta fito a cikinsu da suka Garinmu Da Zafi, ‘Yar Agadez, Ga Duhu Ga Gaske da kuma Walijam sun matukar nunata a idon Duniya, musamman Garinmu Da Zafi wanda ya zama zakaran gwajin dafi a cikin fina-finan Hausa na masana’antar Kannywood a wancan lokacin, Zainab tana daga cikin manyan jarumai mata da suka zamo abin koyi ga kananan jarumai masu tasowa a masana’antar ta Kannywood.