Home Back

Yadda Aka Kafa Tarihi A Gasar Firimiyar Ingila Da Aka Kammala

leadership.ng 2024/7/3
Tarihi

An kammala gasar Premier League ranar Lahadi 19 ga watan Mayu da wasa 10 a filaye daban daban a kuma lokaci daya wanda hakan ne ya kawo karshen wasannin kakar wasa ta 2023 zuwa 2024. Wannan ita ce daya daga babbar gasar kwallon kafa ta Ingila da ba a taba yin irinta ba a tarihi – ga jerin wasu abubuwan tarihin da aka yi.

Cin kwallaye:
Kenan an zura kwallaye 1,246 a kakar da aka kammala, sai dai a kakar wasa ta 1992 zuwa 1993 wadda aka yi wasanni 462, an ci kwallo 1,222, kenan duk da haka an fi zura kwallaye a wannan kakar idan aka kwatanta da ta shekarar.

Dan wasan Manchester City, Erling Haaland shi ne kan gaba a cin kwallaye a bana, wanda yake da 27 a raga kuma a bara shi ne ya lashe takalmin zinare a matakin wanda ya zura kwallaye da yawa a raga mai 36 jimilla.

Ga kuma Jerin wadanda suka fi zura kwallaye a raga:
Erling Haaland Manchester City 27. Sai Cole Palmer 20 Chelsea 22, sannan Aledander Isak Newcastle United 21. Ollie Watkins Aston Billa 19. Dominic Solanke Bournemouth 19. Mohamed Salah Liberpool 18. Heung-min Son Tottenham 17. Phil Foden manchester City 19. Bukayo Saka Arsenal 16. Jarrod Bowen West Ham United 16.

Wadanda ke kan gaba a cin kwallo a kakar wasa ta 2022 zuwa 2023.
Erling Haaland Manchester City 36, sannan Harry Kane Tottenham 30. Iban Toney Brentford 20. Mohamed Salah Liberpool 19. Callum Wilson Newcastle United 18
Marcus Rashford Manchester United 17. Martin Odegaard Arsenal 15. Ollie Watkins Aston Billa 15. Gabriel Martinelli Arsenal 15. Semenyo, Bournemouth.

Cin kwallaye na kayatar da wasan kwallo, kuma a kakar nan an ci wasa a karawar da ake tsammani kungiya za ta yi rashin nasara, amma daga baya ta lashe fafatawar, inda aka yi haka har sau 62.

Karon farko da aka samu wannan kwazon tun da aka fara gasar Premier League a tarihin wasannin daga 2008 zuwa 2009, sannan an kuma farke kwallo a wasa sau 223, karo na biyu a wannan kwazon a gasar ta Premier League tun bayan 237 da aka yi a 1993 zuwa 1994.

Raba kwallo tsakanin ‘yan wasa kan taimaka wa kungiya wajen mamaye gasa, yana kuma nuna kwazo da kwarewar ‘yan kwallo da kociyan dake jan ragamar wannan kungiya.
An bayar da kwallo zuwa abokin wasa kamar yadda ya kamata kaso 83 cikin 100, wato passing, wannan ita ce bajinta ta farko daga kakar wasa 16 tun daga kakar wasa ta 2008 zuwa 2009.

Aston Billa ta zama kungiya ta takwas daga Premier League a kaka uku baya da ta samu gurbin Champions League, ba cikin wadanda suka saba zuwa wasannin gasar ba.

Yadda aka yi neman lashe Premier League
A karo na uku kenan a jere ake fayyace wadda za ta lashe Premier League a ranar karshen gasar, kuma karo na 10 a tarihi kuma makin da yake raba kungiya ta daya da ta biyu baya wuce 1.51, sai dai tun daga 1992/93 ba a samu tazarar maki mafi karanci ba tsakayin ta daya da ta biyun teburin ba. Kungiyoyi bakwai ne suka ja ragamar teburin Premier League a kakar nan.
Kwanakin da kungiya ta yi a saman teburin Premier a kakar wasa ta 2023 zuwa 2024 Liberpool kwana 87, Arsenal kwana 76, Man City kwana 76, Tottenham kwana 26, Brighton kwana 7, Newcastle kwana 7, West Ham kwana 2, An samu matasa da yawa da suka fara buga Premier League a bana.
‘Yan wasan waje ke bayar da gudunmuwa da yawa a gasar Premier League, sai dai wannan karon a samu matasa 61 da suka fara yin kakar bana da su, karo na uku da aka samu da yawa kenan.

Haka kuma ‘yan wasan Ingila sun ci kwallo 359 a bana a gasar da suka zura kwallaye da yawa tun bayan kakar wasa ta 2001 zuwa 2002 – inda ‘yan wasan Ingila shida ke cikin goman farko a yawan cin kwallaye a gasar.

Cole Palmer
‘‘Yan wasa 68 daga kasashen duniya daban-daban ne suka buga Premier League a kakar nan, wadanda ake fara wasa da su a cikin fili tsakanin kungiyoyi 20 da suka kara a bana.
Tun daga sauya fasalin gasar ta Premier League daga shekarar 1992 zuwa 1993, an samu ‘yan wasa 123 daga kasashen duniya da suka buga babbar gasar.

Matsakaicin shekarar ‘yan wasa a kakar nan ya fara daga 26 da kwana 169 kan fara – mafi karancin shekara tun daga kakar wasa ta 2008 zuwa 2009 kuma karo na hudu a karancin shekara a gasar.

’Yan kallo da yawa a filayen wasanni.
Filayen wasa kan dauki ‘yan kallo kaso 98.7 cikin 100 a Premier League ta kakar nan, wadda ta yi kan-kan-kan da tarihin kakar bara kuma daga cikin kungiyoyi 20 da suke buga gasar kakar nan, guda 18 kan samu ‘yan kallo kaso 97 cikin 100. Wasan Liberpool da Tottenham – Premier League. Akwai wasa 10 da aka kalli kai tsaye a talabijin da mutum miliyan uku kowanne suka gani a Burtaniya a kakar nan, kakar da aka fi kallo wadda ta haura ta ita ce kakar wasa ta 2019 zuwa 2020.

Jimilla mutum miliyan 37.7 suka kalli wasa kai tsaye a talabijin da kuma sharhin kwallo na BBC Match of the Day, kimanin kaso 59 cikin 100 a Burtaniya kamar yadda alkaluma suka nuna.

Yadda duniya ke bibiyar Premier League.
Gasar Premier League ta zama mafi girma mai dan karen farin jini a wasan da ake bibiya a Burtaniya da kuma fadin duniya kuma an nuna gasar tsakanin kasashe 189 daga mambobin majalissar dinkin duniya 193 tsakanin gida miliyan 900.

Mutum biliyan 1.87 suke bibiyar Premier League a fadin duniya, wadanda ke tafka muhawara a duk mako a kafar sada zumunta da ta sadarwa, sannan an samu kaso 34 cikin 100 da suke bibiyar Premier League sau da kafa a kaka ta hudu a jere kenan.

Mutane da yawa sun kalli wasa Arsenal da City a Nashville
Wasan Manchester City da Arsenal da aka buga a Premier League ranar 31 ga watan Maris ya zama kan gaba da aka fi kallo a tarihin Amurka, inda mutum miliyan 2.12 da suka kalla a kafar sadarwa ta NBC.
Wasu karin kididigar Premier League
An fara kakar bana daga 11 ga watan Agustan 2023.

Wadanda suka fadi daga kakar bana
Burnley, Sheffield United, Luton Town,
Gurbin Champions League
Manchester City, Arsenal, Liberpool, Aston Billa,
Wasannin da aka buga: 370. Kwallayen da aka ci kawo yanzu: 1,246.
Wanda yake kan gaba a cin kwallaye: Erling Haaland Man City 27 a raga. Fitatcen mai tsaron raga: Dabid Raya (Wasa 16 kwallo bata shiga raga ba)
Wasan da aka ci kwallo da yawa a gida: Chelsea 6–0 Eberton (15
Afirilun 2024)
Wanda aka ci kwallo da yawa a waje: Sheffield United 0–8 Newcastle
United (24 ga watan Satumbar 2023)
Wasannin da aka ci kwallaye da yawa a raga: Sheffield United 0–8 Newcastle United (24 ga watan Satumbar 2023) Chelsea 4–4 Manchester City (12 ga watan Nuwambar 2023). Newcastle United 4–4 Luton Town (3 ga watan Fabrairun 2024). Yawan cin wasa 8 a jere: Arsenal da Manchester City.
Wasa 22 ba tare da rashin nasara ba a jere: Manchester City Wasa 13 ba tare da nasara ba: Eberton da Sheffield United. Wasa shida a jere da rashin nasara: Burnley da Sheffield United. Wasan da ya dauki ‘yan kallo 73,612 Manchester United 3–0 West Ham United (4 ga watan Fabrairu 2024)
Wasan da bai yi mutane ba a filin wasa 10,421
Bournemouth 0–0 Chelsea (17 ga wwatan Satatumba 2023)

People are also reading