Home Back

CBN Ya Bukaci Masu POS Su Yi Rajista Da Gwamnati

leadership.ng 2024/5/20
CBN Ya Bukaci Masu POS Su Yi Rajista Da Gwamnati

Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya bayar da wa’adin ranar 7 ga watan Yuli, 2024 ga masu POS su kammala rajista da hukumar rajistar kamfanoni ta kasa (CAC).

An bayyana hakan ne lokacin da aka yi wata ganawa tsakanin cibiyoyin ada-hadar kudi da shugaban hukumar ta rajistar kamfanoni, Hussaini Magaji a Abuja ranar Talata.

Da yake jawabi a yayin taron, shugaban na CAC ya ce wa’adin watanni biyu na yin rajistar ya yi daidai da ka’idojin doka da kuma umarnin CBN.

Wata sanarwa da CAC ta fitar kuma ta kara da cewa “An dauki matakin ne domin kare masu mu’amala da cibiyoyin hada-hadar kudi tare kuma da karfafa tattalin arziki.

A ranar Talata ne CBN ya bai wa bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudi umarnin fara cire harajin kashi 0.5 daga asusun Kwastomomi domin biyan kudin tsaron yanar gizo.

Sai dai wannan umarni ya tada jijiyoyin ‘yan Nijeriya, lamarin da ya sanya wasu ke ganin an fara kai talaka bango.

People are also reading