Home Back

Dalilin Mayar da 12 ga Yuni Ranar Dimokuradiyya da Buhari Ya Yi

legit.ng 2024/7/7

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - A ranar 6 ga watan Yunin 2018, tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ayyana cewa za a riƙa murnar zuwan ranar dimokuradiyya a Najeriya, a 12 ga watan Yuni maimakon 29 ga watan Mayu.

Buhari ya yi wannan sanarwar ne kwanaki takwas bayan an yi bikin ranar dimokuradiyya na shekarar a ranar 29 ga watan Mayu, wacce ita ce ake amfani da ita kusan shekara 20.

Buhari ya mayar da 12 ga Yuni ranar dimokuradiyya
Buhari ya karrama Cif Moshood Abiola Hoto: Horacio Villaloboss, John Harrington Asali: Getty Images

Ranar 29 ga watan Mayu dai an ayyana ta ne a matsayin ranar dimokuraɗiyya lokacin da aka rantsar tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, a ranar 29 ga watan Mayun 1999.

Muhimmancin ranar 12 ga Yuni

Ranar 12 ga watan Yuni tana da muhimmanci a tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya. A wannan ranar ne a shekarar 1993 aka gudanar da zaɓen shugaban ƙasa tun bayan juyin mulkin shekarar 1983.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An bayyana zaɓen a matsayin wanda aka gudanar cikin gaskiya da kwanciyar hankali a tarihin Najeriya.

Kusan ƴan Najeriya miliyan 14 suka fito suka kaɗa ƙuri'unsu ba tare da nuna bambancin addini da ƙabila ba domin kawo ƙarshen mulkin soja.

Sai dai, an soke zaɓen na ranar 12 ga watan Yunin 1993 wanda ake tunanin cewa Cif Moshood Abiola ne ya lashe.

Buhari ya mayar da 12 Yuni ranar dimokuraɗiyya

Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ayyana ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar dimokuraɗiyya a ranar 6 ga watan Yunin 2018.

Ga wasu daga cikin dalilan:

1. Tunawa da kafuwar dimokuraɗiyya

Tsohon shugaban ƙasa ya ayyana ranar ne domin yin duba kan tarihin ginuwar dimokuraɗiyya a ƙasar nan tare da karrama waɗanda suka yi fafutuka domin samun ta.

Tarihin kafuwar dimokuraɗiyya a Najeriya bai cika ba tare da an ambato ranar 12 ga watan Yuni ba, saboda muhimmancin da take da ita a fafutukar komawa mulkin farar hula a ƙasar nan.

2. Karrama Moshood Abiola

Muhammadu Buhari ya sauya ranar ne domin karrama Cif Moshood Abiola da sauran waɗanda suka rasu a fafutukar ganin an koma mulkin farar hula a Najeriya, cewar rahoton jaridar Premium Times.

Bayan sauya ranar, Buhari ya kuma ba da babbar lambar yabo ta ƙasa ta GCFR ga Cif Moshood Abiola, sannan ya sauya sunan filin wasan ƙwallo na ƙasa da ke Abuja, zuwa filin wasa na Moshood Abiola.

Buhari ya kuma ba mataimakinsa wanda suka yi takara a zaɓen, Babagana Kingibe, lambar yabo ta GCON tare da lauya ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin bil'adama, Gani Fawehinmi.

Buhari ya taya Tinubu murna

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya taya magajinsa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu murnar cika shekara ɗaya a kan karagar mulkin Najeriya.

Buhari ya kuma yi kira ga ƴan Najeriya su marawa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu baya domin ta samu nasarar kai ƙasar nan zuwa ga tudun mun tsira.

Tsohon shugaban ƙasan ya yi kira ga ɗaukacin ƴan Najeriya da su haɗa kai wuri guda kuma su zama masu fatan alheri ga ƙasarsu tare da yi wa gwamnatin Tinubu addu'ar nasara.

Asali: Legit.ng

People are also reading