Home Back

Gobara Ta Tashi a Gidan Tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau

legit.ng 2024/5/20

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - An samu tashin gobara a gidan tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, a ranar Lahadi da daddare.

Gobarar wacce ta auku a gidan tsohon gwamnan da ke Mundubawa, ta lalata ɗakin matarsa ta uku, Halima Shekarau.

Gobara ta tashi a gidan Shekarau
Gobara ta tashi a gidan Malam Ibrahim Shekarau da ke Kano Hoto: @Fedfireng Asali: Facebook

Jaridar Leadership a rahoton da ta fitar ta ce ba a iya gano musabbabin tashin gobarar ba wacce ta fara a ɗakin girkin gidan cikin daren ranar Lahadi.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, mai ba Shekarau shawara kan harkokin yaɗa labarai, Dakta Sule Ya’u Sule, ya ce gobarar ta tashi ne a ɗakin girki na cikin gidan da ke a ƙasan gidan na miliyoyin Naira.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Muna godiya ga Allah gobarar kawai ta shafi ɗaya daga cikin ɗakunan Malam Ibrahim Shekarau ne kuma tuni jami'an hukumar kashe gobara sun kashe ta."

- Dakta Sule Ya'u Sule

Kakakin hukumar kashe gobara, Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma bai yi ƙarin bayani ba kan dalilin tashin gobarar.
"Har yanzu muna cikin gidan sannan ka san ba zan iya yin magana a kan komai ba yanzu saboda muna ta ƙoƙarin ganin cewa gobarar ba ta yaɗu ba zuwa sauran wurare."

- Saminu Yusuf Abdullahi

Asali: Legit.ng

People are also reading