Home Back

An fara taron jana'izar tsohon shugaban Iran

bbc.com 2024/9/28
....

Asalin hoton, REX/SHUTTERSTOCK

An fara taron jana’izar tsohon shugaban Iran, Ibrahim Raisi da sauran mutane bakwan da suka rasu tare, a birnin Tehran.

Ana sa ran manyan baƙi daga sassan duniya za su halarci jana’izar, wadda jagoran addinin Iran Ayatollah Khamenei zai jagoranta.

Yau ranar hutu ce a Iran, kuma ɗaya daga cikin ranaku biyar na zaman makokin rashin tsohon shugaban ƙasar da ya rasu ranar Lahadi, tare da wasu jami’ai bakwai.

Jagoran addinin Iran, Ayatollah Khamenei ɗan shekara 85 ne zai jagoranci jana’izar mutanen takwas da safiyar yau.

Za a zagaya da gawarwakin mutanen takwas a sassan birnin, cikin akwatunan da aka yiwa kwalliya da tutar Iran, daga baya kuma a ajiye su a dandalin Azadi.

Kamar dai yadda aka yi jiya, yau ma ana sa ran dubun dubatan masu alhini su yi jerin gwano a kan titunan birnin har zuwa dandalin Azadi.

Zagayen na bankwana da gawar tsohon shugaban ya ɗauki wani salo na siyasa, inda masu ra’ayin riƙau dake mulkin ƙasar ke fatan yin amfani da lokacin wajen nuna haɗin kai da neman goyon bayan jama’a.

Ana kuma yaɗa hotuna da bidiyon abubuwan da ke faruwa a sassan ƙasar, musamman a shafukan sada zumunta, yayin da yan sanda ke gargadi a kan yada labaran karya da na cin mutumci.

People are also reading