Home Back

“Abin Da Ake Zargin Ɗan Jarida Shuaibu Mungadi Ba Gaskiya Ba Ne”

leadership.ng 2 days ago
“Abin Da Ake Zargin Ɗan Jarida Shuaibu Mungadi Ba Gaskiya Ba Ne”

Shuaibu Mungadi babban ɗan jarida da ke aiki a gidan telebijin na Farin Wata ya tsinci kansa a wani mummunar yanayi, biyo bayan da wata kafar labarai a Jihar Zamfara ta ruwaito cewa ana zarginsa da yi wa ƙawar ƴarsa ciki.

Wannan labari ya ɗauki hankalin mutane kasancewar hakan abu ne da zai ɓata sunansa a cikin al’umma.

Wani bincike da kafar ta yaɗa da ake zargin daga wasu ƴan siyasa ne waɗanda ke harin mutanen da suka saɓa da su wajen ra’ayi, ya ce, Mungadi ya ƙulla mummunar alaƙa da ƴar Maijidda Labaran wanda haka ta kai ga yarinyar ta samu juna-biyu na wata uku.

Kafar ta ce Mahaifiyar yarinyar mai suna Maijidda Labaran, ta ce Mungadi ya yi amfani da damar kasancewarta ƙawa ga ƴarsa ta biyar.

A wani ɓangare kuma, binciken jaridar ‘Spectacles’ ya ce hoton da aka samu a rahoton ya ƙaryata zargin tare da nuna ƙarara hakan kasuwanci ne da kuma yaudara ta siyasa, don maganganu ne da ba su da hujja sai dai kawai hakan wani makirci da kuma yunƙurin ɓata masa suna daga ƴan siyasa da yake ƙalubalantar munanan ayyukansu.

Jaridar ‘Spectacules’ ta buƙaci Mungadi da ya shigar da duk waɗanda ke da hannu cikin ɓata masa suna ƙara, domin doka ta yi aiki a kansu.

Shuaibu Mungadi shi ke jagorantar shirin ‘idon mikiya’ a gidan telabijin na ‘Farin Wata’ da kuma ‘Vision FM’.

People are also reading