Home Back

Gwamnatin Tarayya Ta Hada Kai da Enugu Domin Sarrafa Rogo Zuwa Sinadarin Fetur

legit.ng 2024/6/26
  • A wani yunkuri na ganin an bunkasa harkar noma, gwamnatin tarayya da ta jihar Enugu sun kulla yarjejeniyar nomar rogo da sarrafa shi
  • Kwamishinan noma na jihar Enugu, Hon. Patrick Ubru ya ce za a sarrafa rogon ne zuwa sinadarin fetur na 'bioethanol' bayan an noma
  • A yayin da aka kaddamar da noman hekta 1,000 a matsayin gwaji, Hon. Ubru ya ce na dauki matakai na tabbatar da nasarar shirin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Enugu - Gwamnatin jihar Enugu ta yaba da hadin gwiwarta da gwamnatin tarayya kan noman rogo da sarrafa shi zuwa sinadarin fetur na 'bioethanol'.

Gwamnati ta ce tana kara habaka noman rogo a jihar domin bunkasa tattalin arziki, tare da taimakawa wajen magance rashin aikin yi da rashin tsaro.

An fara sarrafa rogo zuwa sinadarin fetur a Enugu
Hadakar gwamnatin tarayya da jihar Enugu kan sarrafa rogo zuwa sinadarin fetur ta yi nasara. Hoto: Pituk Loonhong Asali: Getty Images

Kwamishinan noma, Hon. Patrick Ubru ne ya bayyana haka a Okpanku da ke karamar hukumar Aninri, jaridar The Guardian ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"An noma hekta 1,000 na rogo" - Ubru

Hon. Ubru ya zagaya da wata tawagar gwamnatin tarayya zuwa kamfanonin da ke aikin sarrafa rogo zuwa 'bioethanol' a kananan hukumomin Aninri, Isi-Uzo da Udi na jihar.

Ubru ya sanar da tawagar ce an noma sama da hekta 1,000 na rogo a kananan hukumomin uku a shekarar da ta gabata, wanda aka yi amfani da shi matsayin gwaji na shirin sarrafa rogo zuwa sinadrin fetur.

Ya kuma bayyana cewa kafin a gyara gonakin, ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane sun yi sansanoninsu a wajen inda suke farmakar mazauna kananan hukumomin.

"Za a gina tituna a garuruwan" - Ubru

Ubru ya ce gwamnatin jihar na kokarin hada kai da gwamnatin tarayya domin kafa sansanin soji a Isi Uzo, yayin da kuma za ta kafa rundunar tsaro ta dakarun gona domin ba da tsaro a gonakin.

Jaridar Leadership ta ruwaito kwamishinan ya kuma bayyana cewa jihar za ta fara aikin gina hanyoyin shiga gonaki masu nisan kilomita 20 a Okpanku.

Ya kara da cewa jihar ta biya kashi 50 cikin 100 na aikin gina titi mai tsawon kilomita 22 daga Ikem a yankin karamar hukumar Isi Uzo zuwa kan iyaka da jihar Benue.

"Abinci zai wadata a Najeriya" - Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito maku cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta tabbatar ta wadatar da 'yan Najeriya da abinci.

Tinubu ya bayyana hakan ne a jihar Neja yayin kaddamar da ginin tituna yana mai cewa gwamnati ta dauki matakai na ganin an inganta noma a fadin kasar.

Asali: Legit.ng

People are also reading