Home Back

Kebbi BSC ta lashe gasar kwallon yashi ta Najeriya karo na uku

premiumtimesng.com 2024/8/21
Kebbi BSC ta lashe gasar kwallon yashi ta Najeriya karo na uku

Kungiyyar kwallon yashi ta Kebbi BSC ta zama gwarzuwar gasar kwallon yashi ta Nijeriya ta 2023/2024 da aka fafata.

Wannan dai shi ne karo na uku da ƙungiyyar take yin irin wannan bajintar.

Kafin hakan dai ta taɓa lashe gasar a shekara ta 2021,2023 da kuma 2024 a dukkanin gasannin Nijeriya huɗu da aka shirya a tarihi.

Kebbi BSC ta samu nasara ne a wasanni kungiyyoyi huɗu da aka buga a filin wasa na Murtala Muhammad dake birnin Kaduna a ranar Lahadi.

Kungiyar ta samu nasara ne bayan karewa a mataki na ɗaya da maki shida cikin wasanni uku da ta buga.

Kungiyoyi huɗu ne dai suka kawo wannan matakin na ƙarshe, bayan buga wasannin zagaye na farko dana biyu da a watan Mayu.

Kungiyoyin da suka fafata a wannan zagayen sun haɗa da Kebbi BSC, Kebbi United, Kada BSC da kuma Anambra BSC.

Bayan fafatawar, Kebbi BSC wacce ta kasance zakarar gasar ta bana, ta ƙare a mataki na farko da maki shida, Anambra BSC ta biyu da maki huɗu, Kebbi United ta uku da maki 3 sai kuma Kada BSC ta huɗu da maki ɗaya.

Zakaran gasar ta bana Kebbi BSC ta samu kyautar Naira ₦600,000, ta biyu Anambra BSC ₦400,000, sai Kebbi United ta uku ₦300,000 sai kuma Kada BSC ta huɗu da ta samu kyautar ₦200,000.

Daga: Muhammad Suleiman Yobe

People are also reading