Home Back

Ƴancin Ƙananan Hukumomi Zai Taimaka Wajen Magance Matsalolin Tsaro – COAS

leadership.ng 2024/10/5
Ƴancin Ƙananan Hukumomi Zai Taimaka Wajen Magance Matsalolin Tsaro – COAS

Babban Hafsan Sojin ƙasa (COAS), Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ya tabbatar da cewa bayar da cikakken ‘yancin cin gashin kai ga ƙananan hukumomi zai taka muhimmiyar rawa wajen magance matsalolin tsaro a Nijeriya. Da yake jawabi yayin bikin Sojojin Nijeriya a garin Jos na jihar Filato, Janar Lagbaja ya jaddada muhimmiyar rawar da ci gaban ƙasa ke takawa wajen magance matsalolin rashin tsaro.

Ya yi tambaya kan dalilin da ya sa masu faɗa a ji ke ƙin amince wa da cin gashin kan ƙananan hukumomi, wanda yawancin ‘yan ƙasar ke buƙata, ya kuma bayyana cewa ‘yancin cin gashin kan ƙananan hukumomi na da matuƙar muhimmanci wajen kawo ci gaba a matakin farko.

Ya yi nuni da cewa kafa kwamitoci ko ma’aikatun gwamnati kawai ba zai wadatar ba, ya kuma bayyana buƙatar samar da ingantaccen shugabanci a matakin ƙananan hukumomi domin daƙile matsalar rashin tsaro.

Janar Lagbaja ya yi nuni da taɓarɓarewar tsaro musamman a yankin Arewa maso Gabas, inda ya kwatanta sauƙin tafiye-tafiye a baya da matsalolin da ake fuskanta a halin yanzu sakamakon rashin shugabanci na gari a matakin ƙananan hukumomi. Ya jaddada cewa wannan batu ya wuce yankin Arewa maso Gabas zuwa Arewa ta Tsakiya da sauran yankunan Nijeriya.

Duk da ƙin amincewa da cin gashin kan ƙananan hukumomi da gwamnonin jihohi suka yi a baya, gwamnatin tarayya na ci gaba da bin matakan bai wa ƙananan hukumomi ‘yancin cin gashin kansu.

People are also reading