Home Back

Da Ɗumi-ɗumi: An Kashe Babban Kwamandan Sojoji A Katsina

leadership.ng 2024/5/14
Da Ɗumi-ɗumi: An Kashe Babban Kwamandan Sojoji A Katsina

An kashe wani babban kwamandan sojoji a wani harin kwantan bauna da yammacin ranar Alhamis a jihar Katsina.

Lamarin dai ya faru ne a kauyen Malali da ke karamar hukumar Kankara a jihar Katsina, inda kwamandan wanda Manjo ne a rundunar sojin Nijeriya ya amsa kiran gaggawa.

A cewar wata ingantacciyar majiya, babban kwamandan na kan hanyarsa ne domin tallafa wa dakarun yankin da suka dakile harin ‘yan bindiga a lokacin.

“Yankin da ke kan titin Zangon Pawa, inda kauyen Malali yake, yana fama da matsalar ‘yan bindiga ”.

“Sauran jami’an soji da ke Malali ne suka nemi karin taimako daga sansanin Maraban Dan’Ali da ke kusa, nan da nan, Manjo  ya yi gaggawar kawo dauki, inda a hanyarsa acikin motar Hilux ‘yan bindigar suka yi masa kwanton bauna suka kashe shi”. Inji wata majiya

People are also reading