Home Back

Cikin yara 10 a Najeriya, 4 na aikin ƙarfi da wahala – NBS

premiumtimesng.com 2024/5/12
Cikin  yara 10 a Najeriya, 4 na aikin ƙarfi da wahala – NBS

Sakamakon binciken da hukumar kididdiga ta kasa NBS ta gabatar ya nuna cewa cikin yara 10 a Najeriya, 4 na aikin ƙarfi da wahala.

Hukumar ta gabatar da sakamakon binciken mai taken ranar Alhamis a Abuja.

Bisa ga sakamakon, binciken ya nuna cewa yara kashi 39.2% ne ke aikin ƙarfi da wahala a ƙasar.

Sakamakon bincike ya kara nuna cewa tilasta yara yin aikin ƙarfi ya zama ruwan dare a Najeriya domin akwai kashi 39.7% na yara masu shekaru 5 zuwa 14 da kashi 37.3% na yara masu shekaru 15 zuwa 17 dake aikin ƙarfi da wahala.

“A takaice dai sakamakon binciken na nuna cewa akwai yara kashi 39.2% masu shekaru 5 zuwa 17 ko Kuma hudu cikin yara 10 wato, kashi 37.3% masu shekara 15 zuwa 17 dake irin waɗannan ayyuka na wahala a Najeriya.

Rahoton ya nuna cewa adadin yawan yara da ke irin waɗannan ayyuka sun fi yawa a karkara fiye da waɗanda ke zaune a birane.

Kashi 62.4% na yara masu shekara 5 zuwa 17 na zama ne a yankin karkara a Najeriya.

Bayan haka sakamakon binciken ya nuna cewa Kudu maso Gabas da Arewa maso Gabas ne suka fi yawan yaran da ke irin waɗannan ayyuka.

Kudu maso Gabas na da kashi 49.9% sannan kashi 49.4% a Arewa maso Gabas.

Binciken ya nuna cewa an ƴaƴan talakawa ne suka fi yawa a wannan matsala samman ya fi muni a gidajen da ake samunƙarancin ilimi

Kashi 94% na irin waɗannan yara suna aiki ne na hannu, kashi 24.2 na aikin, albashi sannan kashi 11.3% na aikin boyi-boyi.

People are also reading