Home Back

EFCC ta Bankado Alakar Tsohon Minista Hadi Sirika da Kamfanin da ya yi Badakalar Kwangila

legit.ng 2024/7/6
  • Hukumar hana yi wa tattalin arziki ta'adi ta bayyana wa kotu cewa diyar tsohon minista Hadi Sirika na cikin badakalar kwangila ta N1.14bn da ake zargin an tafka
  • Shaidar hukumar EFCC na biyu Mishelia Arhyel ya shaidawa kotu cewa kamfanin Al-Buraq Global Investment Ltd da ya y i aikin kwangilar mallakin Fatima Sirika ne da mijinta
  • Mista Arhyel ya ce kamfanin Al-Buraq ya yi rajista a 17 Yuni, 2021 inda aka lissafa daraktocinsa da Jalal Hamma, da diyar tsohon minista Fatima Sirika, da Shinade Saratu

Abuja-Hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta bayyana wa kotu cewa diyar tsohon minista harkokin sufurin jiragen sama, Hadi Sirika na da hannu cikin zargin badakalar kwangila na N1.14bn da ake yi masa.

Shaidan da EFCC ta gabatar a gaban kotu ya bayyana cewa diyar tsohon ministan, Fatima da mijinta Jalal Hamma ne mamallaka kamfanin Al-Buraq Global Investment Ltd da ake zargi da badakalar.

Sirika
EFCC ta ce diyar tsohon minista Hadi Sirika ce mai kamfanin da ake zargi da badakalar kwangilar N1.14bn Hoto: Hadi Sirika, EFCCOfficial Asali: Facebook

Leadership News ta tattaro cewa shaidan da ya kula da harkokin bankin Zenith mai suna Mishelia Arhyel shi ne shaida na biyu da EFCC ta gabatar wa kotu a shari’ar zargin badakala da ta ke zargin Hadi Sirika, ‘yar sa Fatima da sirikinsa Jalal Hamma da kamfaninsu Al-Buraq Global Investment Ltd da aikatawa.

EFCC ta zargi Sirika da azurta kansa

Hukumar EFCC dai ta na zargin tsohon minister Hadi Sirika da azurta kansa da makusantansa ciki har da kamfanin Tianaero Nigeria Limited da Al-Buraq Global Investment Ltd da ake zargin mallakin diyarsa da mijinta ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi zargin Sirika ya bi ta bayan fage wajen bayar da kwangilar aikin jirgin saman Najeriya na Nigerian Air da aikin filin jirhin Katsina da kamfanin Al-Buraq ya yi a kan N1.4 billion, kamar yadda The Cable ta wallafa.

Shaidar EFCC din, Arhyel ya yi ce kamfanin Al-Buraq ya yi rajista a 17 Yuni, 2021 inda aka daraktocinsa su ka hada da Jalal Hamma, Fatima Sirika, da Shinade Saratu.

Dukkanin wadanda ake zargi sun musanta tuhume-tuhumen amfani da kudin jama’a ba bisa ka’ida.

Bayan sauraren shari’ar, kotu karkashin mai shari’a Sylvanus Oriji ta dage ci gaba da sauraron karar zuwa 20 Yuni, 2024.

Kotu ta bayar da belin Hadi Sirika

A wani labarin kun ji cewa kotu ta bayar da belin tsohon ministan sufuri Hadi Sirika da diyarsa da wasu mutane uku da ake zargi da badakala.

Hukumarh ana yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati ta EFCC ce ta bayar gurfanar da tsohon ministan da wasu kamfanoni biyu gaban kotu.

Asali: Legit.ng

People are also reading